Mambobin Jam'iyyar NNPP Sun Fito Zanga-Zanga Kan Sabon Kwamishanan Yan Sandan Da Za'a Tura Kano
- Wasu mambobin jam'iyyar NNPP sun tafi zanga-zanga hedkwatar hukumar yan sanda a Kano
- Yan siyasan karkashin jagorancin tsohon dan takaran Sanata sun ce ana shirin turo sabon kwamishana jihar
- Yau dai saura kwanaki uku zaben gwamnonin Najeriya kuma ta jihar Kano na cikin masu zafi
Kano - Mambobin jam'iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, NNPP, a jihar Kano sun fito zanga-zanga kan zargin cewa hukumar yan sanda na shirin tura wani sabon kwamishanan yan sanda Kano.
Wannan kwamishana mai suna, Balarabe Sule, da NNPP ke zanga-zanga kansa, tsohon dogarin gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ne.
Tsohon Sakataren hukumar TetFund, Baffa Bichi, ne ke jagorantar wannan zanga-zanga.
DailyNigerian ta ruwaito cewa mabiya jam'iyyar NNPP sun taru gaban hedkwatar hukumar yan sanda dake titin BUK domin bayyana rashin amincewarsu.
Jaridar ta kara da cewa majiyoyi sun nuna za'a tura CP Balarabe Sule tare da ACP Abubakar Shika da ACP Adamu Babayo ana saura yan kwanaki zaben gwamnan jihar.
CP Sule gabanin zamansa kwamishanan yan sanda ya kasance mataimaki mai kula da tafiyan lamuran yan sanda a jihar Kano tsawon shekaru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga zamansa kwamishana aka turasa jihar Cross Rivers.
Ga hotunan zanga-zangar:
"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano
Siyasar jihar Kano na cigaba da ɗaukan sabon salo tun bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya. A
cikin irin salon da take ɗauka ne, gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin gwabnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Tasha alwashin kawo tasgaro ga duk wani motsi da jam'iyyar NNPP Zatayi maras kyau yayin zaɓen dake zuwa na Gwabnoni da yan majalisu a jihara ranar 11 ga watan Maris 2023.
Asali: Legit.ng