Tsohon Dan Majalisar Dokokin Jihar Oyo Okunola Ya Mutu Bayan Ya Yi Fama Da Rashin Lafiya
- Tsohon dan majalisar dokokin jihar Oyo, Tirimisiyu Okunola, ya kwanta dama
- Dan uwan marigayin, Bashir Okunola, ya bayyana cewa yayan nasa ya mutu ne sakamakon ciwon siga
- Okunola wanda ke jin radadin mutuwar dan uwan nasa ya tabbatar da da lamarin a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook
Allah ya yi wa tsohon dan majalisar dokokin jihar Oyo, Tirimisiyu Okunola, rasuwa.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa kanin marigayin, Bashir Okunola ne ya sanar da labarin mutuwar tsohon dan majalisar a ranar Lahadi, 5 ga watan Maris, 2023 a shafinsa na Facebook.
Abun da ya yi sanadiyar mutuwar Okunola
Okunola ya wakilci mazabar Ido na jihar tsakanin 2007 da 2011 karkashin inuwar jam'iyyar All Nigeria People’s Party (ANPP), sannan daga baya ya sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An tattaro cewa marigayin ya mutu ne sakamakon lalurar ciwon siga.
Da yake martani kan lamarin, kanin marigayin ya je shafinsa na Facebook inda ya tabbatar da mutuwar dan siyasar.
Ya rubuta a shafinsa:
“Haaaaa yaya me yasa ka tafi ka barmu kwatsam Hon. Tirimisiyu Olasupo Okunola.
Dan marigayi Sani Abacha ya kwanta dama
A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya karbi ran Abdullahi Abacha, daya daga cikin 'ya'yan marigayi shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha.
Marigayi Abdullahi mai shekaru 34 a duniya ya amsa kiran mahaliccinsa a ranar Asabar, 4 ga watan Maris a cikin barcinsa, kamar yadda yayarsa, Gumsu Sani Abacha ta wallafa a shafinta na Twitter.
Tuni aka yi jana'izarsa a makabartar Gudu da ke babban birnin tarayya Abuja bayan an sallaci gawarsa a babban masallacin Juma'a na Abuja.
Shugaba Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Sani Abacha kan mutuwar dansu
Har ila yau, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 4 ga watan Maris, ya mika sakon gaisuwar ta'aziyya ga Hajiya Maryam Sani Abacha a kan babban rashi da ta yi na danta.
Da yake addu'an Allah ya ji kan matashin, shugaban kasar a wata sanarwa daga kakakinsa, Mallam Garba Shehu ya roki Allah da ya baiwa iyalan marigayi Abacha juriyar wannan rashi da suka yi.
Asali: Legit.ng