Yan Sanda Sun Cafke Ɓarayi 50 da Suka Sace Kaya a Gobarar Kasuwar Maiduguri.
- Kasuwar Monday Market Ta Maiduguri Ta Hadu Da Ibti'la'in Gobara ne Da Tayi Sanadiyyar Ragargazar Dukiya Ta Maduden Miliyoyin Nairori a Ranar Lahadi 26 Ga Watan Fabrairu, 2023.
- A Cikin Masu Zuwa Kashe Wuta Da Jaje, Wasu Sun Buge da Guzuma Sun Harbi Karsana, Inda Aka Kama 50 a Cikin su, Dauke Da Kayan Sata.
- Tuni Dai Gwamna Zulum Ya Bada Umarnin A Sake Gina Kasuwar Bayan Kafa Wani Kwamiti da Zai Soma Aikin A Cikin Satin nan
Ana ta Kai wa yake ta kaya. Zance ake na gobara, masu shaguna ƙokarin kashe wuta suke.
Amma daga wani ɓangaren kuma mutane ne suka shigo kasuwa ba don komai ba sai don yin sata, idan suka samu dama.
A cikin masu zuwa ɗaukar kayan ne, Allah ya bawa yan sandan jihar Borno damar kama mutane hamsin da suka shigo domin yin sibaran - nabayye da kayan mutane.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Biyo bayan gobara data ragargaji kasuwar Monday Market ta Maiduguri a ranar Lahadi 26 ga watan Fabrairu na 2023.
Hakan yasa yake holin waɗanda ake zargi a gaban yan jarida, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Borno, Sani Kamilu Shatambaya inda ya shaidawa manema labarai cewar:
Waɗanda ake zargin an kama su ne dumu dumu a cikin harƙalla lokacin da sukai basaja da sunan kashe wutar yayin gobarar.
A cikin waɗanda akayi holin nasu, harda wani yaro dan shekara 20 da yake da alaƙa da lalatawa sojojin sa-kai na Civilian JTF mota kirar Hilux mai lambar rijista 001 wacce take da alaƙa da sashi na 3 na rundunar.
Kakakin hukumar ƴan sandan ta jihar Borno ya tabbatar wa mutane cewa, yan sanda zasuyi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kawo duk wani mai aikata laifi gaban ƙuliya, domin ya girbi abinda yake shukawa kamar yadda TVC News suke ruwaito.
Bola Tinubu Zai Yi Kaura Zuwa Defence House Na Gwamnati da Ke Abuja
Bola Ahmed Tinubu zaiyi ƙaura daga gidan da yake rayuwa yanzu zuwa Defence House dake mallaki ga Gwamnatin Najeriya a Abuja.
Hakan na zuwa ne biyo bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban Kasar Najeriya da aka gudanar Asabar ɗin data gabata.
Kamar yadda majiyar mu ta ayyana, wannan kome da Tinubu zaiyi shi ne somin tabi na kama aikin shugabancin ƙasa da Tinubu zai yi a matakin farko.
Asali: Legit.ng