Yau Take Ranar Zabe: An Farmaki Ma’aikatan Wucin-Gadin INEC a Gombe

Yau Take Ranar Zabe: An Farmaki Ma’aikatan Wucin-Gadin INEC a Gombe

  • Ma'aikatan Wucin-Gadin Zaben Sun Bar Ofishin INEC ne Domin Isa Rumfar Zaben Su Batare da Rakiya Ma'aikatan Tsaro ba
  • Yan Tada Zaune Tsayen Sun Jira Su a Hanya Domin Yi Musu Dirar Mikiya, Inda Sukayi Nasarar Dirar Musu
  • Kwamishinan Yan Sanda Jihar Gombe Mr. Oqua Etim, Ya Bayyana Rashin Jin Dadin sa, yayi Alkawarin Hakan Bazata Sake Faruwa Ba.

Gombe - Yau take ranar da yan Najeriya suka dade suna jira na tsawon shekaru hudu domin gudanar da zaben kasa da aka saba duk bayan shekara hudu.

Zaben na bana yazo da sabon salo, kalubale da kuma tashin-tashina wacce ba’a zata ba.

Gwamnati ta takaita yawan kudade dake yawo a hannun jama’a domin hana siyan kuri’u da yan siyasa ke yi, sai kuma zancen hare-hare da ake kaiwa ofisoshin yan sanda dake kudu maso kudu da sauran sassa daban daban na kasar dake fama da matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Ana Gobe Zabe: Jam'iyyar APC ta Dakatar da Babban Yayan Gwamna Sani Bello

Police202
Oqua Etim
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana tsaka da haka ne kuma duk dai a yau din, mahara da ba’a san ko su waye ba suka farmaki wasu ma’aikatan wucin-gadin INEC yayin da suke tunkarar wajen aikin da aka tura su a jihar Gombe.

An dai ruwaito cewar, ma’aikatan na wucin gadin INEC sun tunkari Makarantar firamare ta Tudun Wada dake tsakiyar garin Gombe ne, inda suna cikin tafiya kawai suka ji an musu kwantan bauna.

Yan Sandan Jihar Gombe sun tabbatar da faruwar farmakin da aka gudanar da sanyin safiyar asabar na 25 ga watan 2 na 2023.

Mr. Oqua Etim shine kwamishinan yan sanda na jihar Gombe, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Inda Mr. Oqua Etim ya bayyana takaicin sa akan yadda yan ta’adda zasu dauki makamai suyi yawo sakaka a ranar zabe, tun kafin jami’an tsaro su karaso wajen.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Karfi da Raunin Tinubu, Atiku, Obi, Kwankwaso a Zaben Ranar Asabar

Sannan ya kara bayyana takaicin sa akan yadda aka bari ma’aikatan zaben na wucin-gadi suka bar ofishin hukumar zaben yankin babu rakiyar jami’an tsaro tare dasu.

Mr. Oqua Etim ya bada ba’asi akan lamarin inda ya bayyanawa Zagazola cewa:

“ Su ma’aikatan sunyi kokarin zuwa rumfar zaben ne, domin su shirya kafin sauran abokanan aikin su da suke jiran jami’an tsaro a ofishin INEC.
“Amma sai fusatattun wadanda aka turo da makaman suka yi amfani da wannan dama suka farmake su. Amma mun dauki mataki kwakwkwara domin ganin hakan bata sake faruwa ba.
“Ina mai tabbatar muku cewa haka bai aba faruwa ba. Mun shirya cewa, duk sanda zasu bar ofishin INEC zasu bar wajen ne a dunkule salon tsintsiya madaurinki daya dake shirin yin aikin gayya, sannan kuma ko wacce dunkulalliyar kungiya zamu rakata zuwa rumfar da zatai aikin.

Sanda muke hada wannan rahoto, duk wani kokari da mukayi domin jin ba’asi daga hukumar zabe ta INEC reshen jihar Gombe abin yaci tura.

Kara karanta wannan

Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’

Domin kuwa kakakin hukumar INEC na jihar ta Gombe, Mohorret Bigun baya daga kiran wakilan mu ballantana dawo da kira.

Najeriya a karkashin mulkin Muhammadu Buhari na kokarin ganin tayi sahihin zaben da ba’a taba yin irin sa ba, to sai dai kokarin na haduwa da kalubale iri iri, kama daga kone ofisoshin yan sanda, kai hari ga ma’aikatan zabe dadai sauran su.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida