Jam'iyyar APC ta Dakatar da Sani Bello, Kawu a Wajen Gwamnan Jihar Niger

Jam'iyyar APC ta Dakatar da Sani Bello, Kawu a Wajen Gwamnan Jihar Niger

  • Kasa da Kwana Guda Zuwa Zabe Jamiyyar ta Zargi Kawun a Wajen Gwamnan da Yin Ayyukan 'Anti Party' daka iya kawo wa jamiyyar Matsala a Zaben Gobe
  • Kafatanin Manya na Mazabar Kontagora Sun Amince da Korar Sani Bello Daga Jam'iyyar Abisa Wannan Zargi
  • Masu Ruwa Da Tsaki a Jam'iyyar Sun yi Misali Da Wani Sakin-Layi na Anti-Party da Yayi a Gidan Rediyo Daya Sa Suka Yanke Hukuncin

Neja - Lamurran siyasa na ƙara ɗaukan zafi a kowanne mataki na ƙasar nan a yayin da ake kasa da awanni 24 zuwa zabukan shugaban kasa.

Hakan na daga dalilin da yasa jam'iyyar APC ta jihar Niger ta dakatar Sani Bello wanda aka fi sani da 'Sani Basket' kawu a wajen Gwamnan jihar ta Niger, Abubakar Sani Bello.

Kara karanta wannan

Yadda Tururuwar Mutane Sukayi Farin Dango A Kano Domin Tarbar Kwankwaso

Dakatarwar da aka yi wa kawun na Gwamnan APC dake reshen jihar Naijan, dakatarwa ce irin ta sai-baba-ta-gani.

Niger
Abubakar Sani Bello Hoto: Arewa Reporters
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani Bello dai ana zargin sane da ayyukan "Anti Party" , wanda a cewar jamiyyar zai iya kawo wa jam'iyyar APC matsala a jihar.

Dakatarwa ta samu sahalewa ne biyo bayan matsaya da aka cimma a taron mazaɓar Kontagora ta tsakiya da aka gabatar.

Shugabancin Mazaɓar Kontagora ne ƙarƙashin jagorancin Hamza Majidadi da sakataren sa Alhaji Abdullahi Kira suka sawa dakatarwar hannu.

A wata wasiƙa da Jaridar The Nation tayi ido biyu da ita ta faɗa cewa:

"Mun rubuta wasikar nan zuwa ga shugaban Mazaɓar Kontagora ta tsakiya domin miƙa matsaya da muka cimma ta haɗaka a cikin gida, domin dakatar da Honorabul Sani Bello Mustapha (Basket) daga ayyukan jam'iyya har sai abinda hali yayi.

Kara karanta wannan

An Garƙame Iyakokin Najeriya Domin Gudanar da Babban Zaɓen Ƙasa.

Wasikar ta Kara da Cewa:

"Wannan matsayar haɗaka da muka cimma domin korar wannan ɗan jam'iyyar tamu, mun yita ne saboda ayyukan sa da yake domin kawo faɗuwar jam'iyyar mu wato (aAnti Party)." Inji Wasiƙar.

Jam'iyyar ta APC ta kuma ƙara da cewa Sani Bello Mustapha ya daɗe yana yin zantuka tare da yin ayyuka da suke nuna yana yaƙar jam'iyyar sane, wanda hakan zai iya taɓa wa jam'iyyar muhibba.

Saboda haka ne Wasiƙar ta bada misali da abu guda daya taɓa faruwa wanda yake dalili ne da zasu iya dakatar dashi.

A cewar Wasiƙar:

"Maganganun dakayi a Landmark FM na ranar 21 ga watan Fabrairu, 2023 shaida ce ƙuraƙwatan dake nuna cewa wannan bawan Allah baya bin dokar kundin tsarin mulkin jam'iyya. Saboda haka, wannan mutumin, (Hon. Sani Bello Mustapha) , mun dakatar dashi babu ranar dawowa dashi cikin jam'iyyar APC."

Gabatowar Zabukan Kasa Yasa Jamiyyu sai garanbawul suke tare da dinke duk wata baraka daka iya sawa a samu nasara ko akasin haka.

Kara karanta wannan

Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’

Masu hasashe da yawa na ganin watakila hakan bai ya rasa nasaba da babu wanda yake so ya fadi zabe duba da zasu iyayin azumi na shekaru hudu kafin sake samun wannan dama.

A inda wasu kuma ke kallon ba komai bane ke sanya ayi haka face bukata irin ta kashin kai datayi yawa a wajen yan siyasan.

Koma dai menene, ba'a sanin maci tuwo ba sai miya ta kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida