Shehin Tijjaniyah, Sheikh Dahiru Bauchi Ya Marawa Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar

Shehin Tijjaniyah, Sheikh Dahiru Bauchi Ya Marawa Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar

  • Sheikh Dahiru ya yi magana game da zaben shugaban kasa na Najeriya da ke tafe a ranar Asabar mai zuwa
  • Malamin na darikar Tijjaniya ya ce, dan takarar shugaban kasa na PDP zai zaba a ranar Asabar 25 ga watan Faburairu
  • Malaman addini na ci gaba da bayyana 'yan takararsu, 'yan siyasa na ci gaba da shirin zaben shugaban kasa

Jihar Bauchi - Sheikh Dahiru Usman Bauchi, shugaban darikar Tijjaniya ya ce, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar zai zaba a zaben ranar Asabar.

Fitaccen malamin ya bayyana goyon bayan Atiku ne a sakon da ya ba mabiyansa, Daily Trust ta ruwaito.

Idan baku manta ba, a ranar Asabar 25 ga watan Faburairu ne za a yi zaben 2023 na shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben jibi: Rudunar soja ta fitar da sako mai daukar hankali ga dukkan 'yan Najeriya

Atiku Abubakar 'yan Tijjaniya za su zaba, inji Sheilkh Dahiru Bauchi
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Batun Sheikh Dahiru Bauchi kan zaben bana

Da yake jawabi, malamin ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba a saran mumini a sau biyu a wuri guda, wasu mutane suna cewa wai a zabi wanda zai ci gaba daga inda suka tsaya, bamu ji dadin inda suka tsaya ba.
“Da yawan mutane na sun ce za su zabi Atiku, nima ba zan bar mutane na ba, zan kasance tare da mutane na don ganin abin da Allah zai yi.
“Muna rokon Allah ya ba Najeriya shugaba na gari wanda zai saukake dukkan kuncin Najeriya da kuma kawo ci gaba.”

Shugaban gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ibrahim Dahiru Bauchi ya tabbatar da wannan matsaya ta Shehi ga jaridar Daily Trust.

Ya zuwa yanzu dai malamai a Najeriya na ci gaba da bayyana matsayarsu game da 'yan takarar da suke son a zaba.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Babban Abinda Ya Sa Atiku Abubakar Zai Iya Rashin Nasara a Zaben Ranar Asabar

Shehu Sani ya caccaki gwamnonin G5

A wani labarin kuma, gwamnonin G5 masu adawa da Atiku sun sha caccaka daga tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani kan sabanin da suka samu na ra'ayi.

Ya bayyana cewa, abin kunya ganin yadda a baya suke nuna tafiya tare, amma suka gaza tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya da suke ya gaji Buhari a zaben bana.

Hakazalika, ya yi tsokaci ga yadda gwamnonin a baya suke tafiya tare, suke sanya sutura iri daya, amma yace duk a banza tunda sun gaza tsayawa a sahu guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.