Zaɓukan 2023: Kimanin N500bn ne Basu Dawo Cikin Babban Bankin Najeriya ba har Yau - Bawa
- Shugaban Hukumar EFCC na Kasa Abdulrasheed Bawa yace Yan Siyasa Sun Ninke Damman Nairori a Gida
- Yace Kimanin Biliyan 500 Har Yau Basu Dawo Cikin babban Bankin Najeriya CBN ba.
- Shugaban Hukumar Ya Kuma ce CBN ta Saki Kudi Kimanin Biliyan N500 Domin Yawo a hannun Mutane
EFCC, Abuja -A yayin da Zabukan 2023 ke kara karatowa, abubuwa sai kara kunno kai suke na daga boyayyun lamurra da suke kaman ceceniya da almara da al'ajabi game da batan dabo da kudaden kashewa suke yi a hannu jama'a.
A mafi yawancin lokaci, yan Najeriya na mamakin shin anya hukumar EFCC na aikin ta kuwa? Ana tsaka da haka ne sai Shugaban Hukumar ya tabbatar da cewar suna sane da duk abinda ke faruwa.
Kuma a shirye suke su kama gamida gabatar da duk wani mai laifi a gaban kuliya manta sabo. Musamman ma yan siyasa masu boye kudi da nufin siyan kuri'ar zabe a 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abdulrasheed Bawa ya furta hakane a wata tattaunawa da yake da gidan talabijin na Channels a safiyar yau.
Shugaban ya ƙara da cewa, hukumar sa baza tayi ƙasa a gwuiwa ba wajen yin dumu dumu da yan siyasan da suke da burin haka ba.
Domin kamar yadda ya faɗa, suna da tarin bayanai sahihai kan ƴan siyasan da suka shirya siyan ƙuri'u da kuɗi duk da canjin da akayi.
A cewar sa
"Hanya daya da suke bi shine su sayi kuri'a. Na'urar nan ta BVAS zata bada mamaki sosai. Saboda haka, zasuyi amfani da kuɗi da suka tara. Muna da rahoto mai tarin yawa da zamuyi amfani dashi akan su. Ina kuma farin cikin sanar damu cewa, dukkan bangarorin tsaro suna bamu haɗin kai domin ganin nasarar zaɓen nan.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito shugaban hukumar yana cewa:
"Tabbas bayanai sun nuna mana wasu mutane suna ɓoye kudi domin siyan ƙuria. Domin a yau, muna da kimanin Naira Biliyan 500 da basu dawo asusun babban bankin Najeriya ba CBN."
Shugaban na EFCC ya ƙara fito da batun ƙarancin kuɗi da ake fama dashi, ta hanyar sanar da cewa, tuni CBN ya bugo kuɗi har biliyan 500, kuma suna nan suna zagayawa.
A cewar sa:
"CBN ya buga kuɗi wuri na gugar wuri har Naira biliyan 500 na sababbin kuɗi, wanda yanzu haka suke hannun al'umma.
Sannan shugaban ya ƙarƙare da cewar, Allah zai taimake su wajen kama masu mugun nufin sayen ƙuri'a da taimakon bayanan sirrin da suke dashi.
Asali: Legit.ng