Bayan Jawabi Ga Yan Najeriya, Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Waje Yau

Bayan Jawabi Ga Yan Najeriya, Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Waje Yau

  • Shugaban Najeriya zai halarci taron shugabannin kasashen nahiyar Afrika a birnin Addis Ababa
  • Buhari a karon farko ya yi jawabi ga yan Najeriya kan lamarin karancin tsabar kudin da ake fama
  • Har yanzu ana cikin sharhi kan jawabin da Buhari ya gabatar, yayinda shi kuma zai tafi kasar waje

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Habasha domin halartan taron gangamin gammayar kasashen nahiyar Afrika karo na 36 da zai gudana a Addis Ababa.

Buhari zai tafi ne yau Alhamis, bayan jawabin da ya yiwa yan Najeriya kan lamarin karancin Naira.

Fadar shugaban kasa a jawabin da ta fitar ta bayyana abubuwan da shugaban kasan zai yi.

Buhari
Bayan Jawabi Ga Yan Najeriya, Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Waje Yau Hoto: Buhari
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jawabin, Shugaba Buhari zai halarci zama daban-daban a tsawon kwanaki hudu da zai kwashe a kasar waje.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

A cewar jawabin:

"Shugaba Buhari a ranar Alhamis za tashi daga Abuja zuwa Addiss Ababa, Ethiopia, domin halartan taron gangamin gamayyar kasashen Afrika karo na 36."
"Shugaban kasan zai halarci taruka uku kan zaman lafiya da tsaro, sauyin yanayi, da kuma tashin-tashinan siyasa a wasu kasashe Afrika ta yamma."

Jerin ganawar da Buhari zai yi a Addiss Ababa

Fadar shugaban kasa tace:

"Na farko shine ganawar shugabannin kasan Afrika kan zaman lafiya da tsaro musamman a kasar Congo karkashin jagorancin Shugaban kasar Afrika ta kudu."
"Na biyu shine zaman kwamitin shugabannin kasa kan sauyin yanayi, wanda ke karkashin jagorancin Shugaban kasar Nijar."
"Bayan zaman gammayar kasashen Afrika, Shugaba Buhari zai halarci zaman shugabannin kasashen yankin ECOWAS."

Ranar dawowarsa

Jawabin ya kara da cewa shugaba Buhari zai samu rakiyar wasu Ministoci da manyan jami'an gwamnati.

A cewar Garba Shehu:

"Zai dawo ranar Litnin, 20 ga watan Febrairu."

Kara karanta wannan

An samu mafita: Ana tsaka da shan wahalar Naira, Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi

Alfanun guda bakwai (7) Da Sauya Fasalin Kuɗi Ya Samarwa Ƴan Najeriya - Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa shirin sauya fasalin takardun naira ya haifar da ɗa mai ido, duk da cewa an samu wasu matsaloli wajen aiwatar da shi.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga yan Najeriya, kan ƙara wa'adin tsofaffin kuɗi, a safiyar Alhamis, 16 ga watan Fabrairun 2023.

Yan Najeriya na martani kan haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida