Karya Ne, Babu Wanda Ya Yiwa Mai Mala Buni Rajamu: Ahmad Lawan
- Sanata Ahmad Lawan ya ce yan adawa ne suka shirya labaran karya cewa na jefi gwamnan jihar Yobe
- Rahotanni sun gabata kan yadda matasa suka yiwa gwamna Mai Mala Buni rajamu a Gashua
- Ahmad Lawan ya yi taron ne matsayin murnar nasarar da ya samu a kotun koli kan Bashir Machina
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karyata rahotannin cewa an tayar da tarzoma a wajen taron kamfen jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Gashua, karamar hukumar Bade ta jihar Yobe.
Mai magana da yawun Ahmad Lawan, Ola Awoniyi ya fitar da jawabi ranar Lahadi a Abuja, rahoton TheNation.
Ya bayyana cewa karerayi kawai yan jarida suka yada cewa an yiwa gwamna Mai Mala Buni jifar shaidan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa:
"Mun samu labarin karya da kagaggu a kafafen yad alabarai game da taron kamfen APC da akayi a Gashua, karamar hukumar Bade ta jihar Yobe, ranar Asabar, 11 ga Febrairu, 2023."
"Rahotannin na cewa an tayar da tarzoma a taron kuma mabiyan wani dan siyasa ne suka kai harin, wanda ya kai an yiwa wasu jagororin jam'iyyar rajamu."
"Muna masu bayyana cewa wannan ba gaskiya bane."
Yan Bindiga Sun Tare Titin Abuja-Minna, Sun Hallaka DPO Da Yan Sanda 4
A wani labarin kuwa, Yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Neja sun kai wasu hare-hare wanda yayi sanadiyar mutuwar DPO na yankin Paiko, Mukhtar Sabou, da wasu yan sanda hudu.
Wannan abu ya auku ne a karamar hukumar Paikoro na jihar.
An bindige yan sandan har lahira ne a kauyen Kwakuti, titin Minna zuwa Suleja ranar Asabar, rahoton DailyTrust.
Asali: Legit.ng