Yan Bindiga Sun Tare Titin Abuja-Minna, Sun Hallaka DPO Da Yan Sanda 4
- Yan bindiga masu garkuwa da mutane na cigaba da karnukansu ba babbaka a arewacin Najeriya
- Rana tsaka yan bindigan da suka addabi al'ummar jihar Neja suka tare babbar hanyar zuwa Abuja
- Rahotanni sun nuna cewa an yi rashin waus jami'an yan sanda da suka yi artabu da su
Yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Neja sun kai wasu hare-hare wanda yayi sanadiyar mutuwar DPO na yankin Paiko, Mukhtar Sabou, da wasu yan sanda hudu.
Wannan abu ya auku ne a karamar hukumar Paikoro na jihar.
An bindige yan sandan har lahira ne a kauyen Kwakuti, titin Minna zuwa Suleja ranar Asabar, rahoton DailyTrust.
Kakakin hukumar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an kashe DPOn da jami'ansa ne bayan artabu da yan bindigan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
"Kimanin karfe 1100hrs, mun samu labarin cewa an ga yan bindiga a wajen Kwakuti-Dajigbe dake Lambata, yayinda suke niyyar kai hare-hare a karamar hukumar Gurara."
"Rundunar yan sanda daga yankin Gawu-Babangida da Paiko, Sojoji, yan bijilante, suk sun dira wajen, sun yi musayar wuta kuma an kashe da dama cikinsu, yayinda wasu suka gudu da raunuka."
A cewar DailyTrust, wani direban motan haya dake bin hanyar, Adamu Usman, ya laburta mata cewa yan bindiga sun tare titin Abuja zuwa Minna tun karfe 10 na safiyar Asabar har na tsawon awani.
A cewarsa:
"Jiya a tashohinmu dake Minna da Jabi a Abuja, babu fasinjoji saboda mutane da dama sun koma gida yayinda suka samu labarin. Kafin na samu fasinja daga Minna zuwa Abuja jiya sai kusan karfe 1."
Asali: Legit.ng