Mun Cika Manyan Alkawura 3 Da Muka Yiwa Yan Najeriya: Buhari

Mun Cika Manyan Alkawura 3 Da Muka Yiwa Yan Najeriya: Buhari

  • Shugaba Buhari ya ce yana godewa Allah ya cikawa yan Najeriya alkawuran da ya musu a 2015
  • Buhari ya ce lokacin da ya hau mulki a 2015 kasar nan na cikin mawuyacin hali amma abubuwa sun yi sauki yanzu

Ekiti - Ana saura kasa da yan watanni wa'adin mulkinsa ya kare, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika manyan alkawura uku da ta yiwa mutane a 2015.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin bikin yaye daliban jami'ar tarayya dake Oye-Ekiti FUOYE, rahoton Tribune.

A cewarsa, gwamnatin ta cika alkawarinta a bangaren tattalin arziki, rashin tsaro da kuma yaki da rashawa.

Buhari
Mun Cika Manyan Alkawura 3 Da Muka Yiwa Yan Najeriya: Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Depositphotos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari ya ce alkawarin da ya yiwa yan Najeriya shine zai inganta tattalin arziki, zai inganta tsaro kuma zai yi yaki da rashawa.

Kara karanta wannan

Fayose Ya Yi Zazzafan Martani, Ya Bayyana Wadanda Ke Da Hannu a Matsalolin Najeriya

Ya ce yana farin ciki saboda ya samu gagarumin nasara a wadannan bangarori guda uku.

A cewarsa:

"Bari in tuna muku na gina kamfe na a 2015 ne kan alkawarin inganta tsaro, karfafa tattalin arziki da yaki da rashawa."
"Ina godewa Allah cewa ina alfahari mun cika wadannan alkawura guda uku."
"Lokacin rantsar da ni, kasar nan na karkashin mulkin yan ta'adda da sauran matsalolin tsaro. Ina alfaharin cewa mun samu nasara kan yan ta'adda kuma mun kwasto dukkan yankunan da suka mamaye."
"Hakazalika karkashin mulki na Najeriya ta farfado da tattalin arzikinta da ya kusan rushewa har zuwa yanzu da kasar ta zama mai tattalin arziki mafi girma a nahiyar Afrika."
"Rashawa ya kusa kashe kasar nan kafin na shiga ofis a 2015. Amma wasu tsare-tsaren da gwamnati na ta samar irinsu TSA, masu cinne (hura usur), da kuma gurfanar da yan rashawa da hukumom ne yi wanda ya rage rashawa a kasar."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam El-Rufai Ta Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan Siyasa Dake Shirin Ta Da Yamutsi

Buhari ya kara da cewa bayan wadannan abubuwa guda uku, gwamnatinsa ta farfado da sashen Ilimi ta hanyar gine-gine da 'daga mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida