Gwamnatin Buhari ta Bukaci Kotun Koli Tayi Watsi Da Karar Gwamnonin Da Suka Shigar Kan Tsaffin Naira

Gwamnatin Buhari ta Bukaci Kotun Koli Tayi Watsi Da Karar Gwamnonin Da Suka Shigar Kan Tsaffin Naira

  • Gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da martani kan hukuncin kotun koli
  • Gwamnati ta ce kotun koli ba tada hurumin sanya baki cikin lamarin shirin daina amfani da tsaffin Naira
  • Saura kwanaki biyu karewar wa'adin da kotun koli ta karawa tsaffin Naira a umurnin da tayi

Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kotun kolin Najeriya tayi watsi da karar da gwamnonin APC suka shiga ne bukatar soke ranar 10 ga Febrairu, 2023 matsayin ranar karshe na daina amfani da tsaffin takardun Naira.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kotun koli ba tada hurumin sauraron karar, rahoton PremiumTimes.

Gwamnonin da suka shigar da kara sune gwamnan jihar Nasir El-Rufa'i, Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Gwamnonin su uku gabatar da bukata gaban kotun koli na a hana da shirin haramta amfani da tsaffin takardun Naira na N1000, N500 da N200 da gwamnatin tarayya da babban bankin tarayya CBN ke kokarin yi a ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Tsoffin Kudi: Gwamna Masari Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Bankuna Da Yan Kasuwa a Jihar Katsina

BUhari
Gwamnatin Buhari ta Bukaci Kotun Koli Tayi Watsi Da Karar Gwamnonin Da Suka Shigar Kan Tsaffin Naira
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, wanda ya mayar da martani kan karar ya ce wannan lamari ba tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi bane, wannan lamarin shiri ne na CBN kawai.

Ya ce saboda haka wannan kara bata cancanci a kaita kai tsaye wajen kotun koli ba. Ya ce babban kotun tarayya ya kamata a fara kai tukunna.

Saboda haka Abubakar Malami ya bukaci kotun koli ta soke hukuncin da tayi ranar Laraba.

Hukuncin da kotun koli tayi ranar Laraba

A ranar Laraba, kotun kolin Najeriya ta dakatad da yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na hana amfani d atsaffin takardun Naira fari da ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Kwamitin Alkalan kotun guda bakwai karkashin jagoranicin Justice John Okoro, ya dakatad da shirin.

Har yanzu gwamnatin tarayya ko CBN basu yi magana kan ko zasu bi umurnin ba ko ba zasu bi ba.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Gwamnatin Jihar Neja Ta Bi Takwarorinta Na Kogi, Kaduna Da Zamfara, Ta Maka Buhari a Gaban Kotu

Sauran kwanaki biyu dai wa'adin 15 ga Febrairu, 2023 ya kare kuma a koma kotu.

Buhari ya kira taron gaggawa na dukkan tsaffin shugaban kasa

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa na majalisar magabatar Najeriya domin tattaunawa kan abubuwan da suka shafi tsadar man fetur, karancin Naira, rashin tsaro da sauransu yayinda ake shirin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida