Rikici Ya Barke a APC na Taraba, An Fitittiki Shugaban Jam'iyya
- Da alamun za'a shiga zaben 2023 amma jam'iyyar APC na fuskantar yakin cikin gida har yanzu
- Rikicin da ya kai ga soke zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar ta sauya zani kuma
- Kotun koli ta soke Emmanuel Bwacha matsayin wanda yayi nasara a zaben fidda gwanin dan takarar gwamna
Jalingo - Rikicin da ya 'dai'daita 'yayan jam'iyyar All Progressive Congress APC na Taraba wanda ya kai ga soke zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar a kotun koli ya dau sabon salo.
Mutum 38 cikin mambobin kwamitin zartaswar jam'iyyar sun tsige shugaban jam'iyyar, Ibrahim El-Sudi, rahoton Punch.
A jawabin da wadannan mambobi suka fitar, sun bayyana cewa sashe na 21(d)(vi) na kundin tsarin mulkin APC yabasu damar tsige shugaban jam'iyya.
Suka ce:
"Dalilin kuri'ar rashin amincewa da El-Sudi da kuma tsigeshi matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar Taraba ya biyo bayan gazawarsa wajen gudanar da ayyukansa."
"Shugaban ya yi watsi da ayyukansa. Sabanin umurnin jam'iyya na cewa ayi amfani da tsarin deleget wajen zaben fidda gwani, shugaban APC na jihar ya turawa INEC cewa yar tinke za'a yi amfani da shi."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wannan ya tada rikici cikin jam'iyya, kuma hakan ya haddasa kai-komo a kotu."
Martanin masoyan El-Sudi
Martani kan lamarin, kakakin jam'iyyar APC na jihar, Aaron Artimas, yace wasu yan tsiraru ne kawai ke ikirarin cire shugaban jam'iyya saboda sun lura ba zasu samu damar yin abinda suke so a zaben fidda gwanin da za'ayi ranar 10 ga Febrairu ba.
A cewarsa:
"Ni mamba kwamitin zartaswa ne, amma ban rattafa hannu kan takardar tsigeshi ba. Kawai abinda suka yi shine kawo mambobin kwamitin masoya David Kente don aikata wannan abin kunya."
Jam'iyyar APC Ta Zabi Ranar Gudanar Da Sabon Zaben Fidda Gwani A Taraba
Uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da ranar gudanar da sabon zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar Taraba a zaben 2023 da zai gudana.
APC ta zabi ranar Juma'a, 10 ga watan Febrairu, 2023 kamar yadda wasikar ya nuna.
Asali: Legit.ng