Kungiyar 'Sight and Sounds' Ta Shirya Taro Kan Manufofin Asiwaju Bola Tinubu
Wata kungiyar kare manufofin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, ta shirya taro na musamman kan fashin baki cikin manufofin dan takaran.
Kungiyar mai suna 'Sight and Sounds of Renewed Hope' ta shirya taron ne wanda ya gudana a dakin taro ba Merit House dake birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 25 ga Junairu, 2023.
Wadanda suka gabatar da jawabai a taron sun bayyana karfafa matasa, samar da ayyukan yi, horar da matasa da inganta kasuwanci a matsayin abubuwan da zasu kawo cigaba matuka ga Najeriya.
Sun yi bayani kan yadda ya kamata a fahimtar da yan Najeriya wasu abubuwa dake cikin takardar manufofin Tinubu musamman bangaren karfafa matasa ta hanyar basu jari na banki cikin sauki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wadanda suka yi jawabi a taron sun hada da Suwaiba Shehu Ibrahi, Malama a jami'ar jihar Kaduna KASU; Dr Ibrahim BM Gaya, mai baiwa gwamnan Kaduna shawara kan raya karkara; da kuma Umar Sani Macho.
Sun bayyana cewa:
"Wani bangare mai muhimmanci na cikin manufofin Tinubu shine samar da cibiyoyin horar da matasa kan ayyukan hannu. Babu yadda zamu cigaba idan matasanmu basu da ayyukan hannun da zai taimaka musu wajen samun aiki da kuma su iya rike kansu."
"Aikin hannu shine mafita, ba kwalin Boko ba. Lallai zuwa makaranta da samun digiri na da muhimmanci amma shi zai magance matsalolin yau da kullum cikin al'umma? ...Bamu bukatar wani yazo daga waje ya magance mana wannan matsalar."
Asali: Legit.ng