Luwadi Ba Laifi Bane: Fafaroma Francis Ya Bayyanawa Duniya

Luwadi Ba Laifi Bane: Fafaroma Francis Ya Bayyanawa Duniya

  • Fafaroma, jagoran al'ummar mabiya addinin Kirista na darikar Katolika ya bada sabuwar fatawa
  • Wannan fatawa ta girgiza yanar gizo inda mutane suka fara bayyana ra'ayoyinsu kan jawabinsa
  • Fafaroma ya bayyana cewa masu auren jinsi basu aikata wani laifi a idon jama'a ba

Shugaban al'ummar cocin Katolika na duniya, Fafaroma Francis ya soki dokokin dake hukunta masu aikata luwadi inda yace Ubangijinsu bai nuna banbanci tsakanin halittunsa.

Fafaroma ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da Associated Press ranar Talata, 24 ga Junairu, 2023.

Yace aikata Luwadi haramun ne a addini amma bai kamata a hukunta wani don ya yi ba.

Ya yi kira ga sauran limaman katolikan duniya su yi maraba da dukkan mutanen dake son zuwa ibada cocin ko da ko yan luwadi ne da madigo.

Paparoma
Luwadi Ba Laifi Bane: Fafaroma Francis Ya Bayyanawa Duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

A cewarsa:

"Zama dan luwadi ba laifi bane."

Ya ce al'adu ne yasa mutane ke kin jinin masu auren jinsi guda. Ya ce idan yin luwadi laifi ne, kyamar wasu don suna aikata wani abu ba laifi ne.

Ya ce daga yanzu wajibi ayi marasa da yan luwadi a cocin katolika kuma a girmamasu ba tare karamci.

Allah Ya Yi Wa Fafaroma Benedict Rasuwa Yana Da Shekaru 95

Tsohon Fafaroma na Katolika, Benedict XVI ya rasu a gidansa da ke Mater Ecclesiae a birnin Vatican.

Kamar yadda Al-Jazeera ta rahoto, Fafaroman ya rasu a ranar Asabar 31 ga watan Disamba.

Rasuwarsa na zuwa ne bayan rahotanni da dama da suka fito a kafafen watsa labarai da ke nuna cewa yana fama da rashin lafiya.

Fafaroma Francis wanda ya tabbatar da rashin lafiyarsa ya bukaci mutane su masa addu'a ya samu sauki yayin da ya bayyana cewa rashin lafiyan ya yi 'tsanani'.

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Sa An Gaza Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Benedict ne fafaroma tun Afrilun shekarar 2005 har zuwa lokacin da ya yi murabus a 2013, abin da ya bawa duniya mamaki.

A cewar New York Times, an fatan za a tafi da gawarsa zuwa St Peter's Basillica a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu inda mabiya darikar katolika za su tarbi gawar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: