Hotunan Yadda Yan Najeriya Suka Cika Bankuna Don Mayar da Tsaffin Kudi
Gwamnan bankin tarayyar Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa ko kadan ba zasu dage wa'adin ranar daina amfani da tsaffin kudaden Naira ba.
Gwamnan ya jaddada cewa ranar 31 ga watan Junairu, 2023 ne ranar karshen amfani da tsaffin takardun kudin N500, N200 da N1000.
Emefiele ya ce ko shugaba Buhari ya amince kwanaki 100 da aka bada don mutane su canza kudadensu ya isa.
Ya bayyana cewa har dajin sambisa akwai kudi saboda sun tura jami'ansu su taimaka wajen canzawa mutane kudaden.
Yayinda ake saura kwanaki 6 yau, yan Najeriya su cika bankuna a arewacin Najeriya suna kokarin ajiye kudaden kafin su zama ruwa.
Hotuna sun nuna yadda wasu suka cika banki har suka kabbarta sallah cikin banki.
Kalli hotunan:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Asali: Legit.ng