Hotunan Shugaba Buhari Inda Ya Samu Lambar Yabon Wanzar da Zaman Lafiya a Afrika
- Shugaba Muhammadu ya tafi kasar Mauritania ranar Litnin zuwa kasar Larabawan Mauritania
- A ranar Talata, an bashi lambar yabo bisa kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya
- Kasar UAE ta tabbatar da rawar ganin da Shugaba Buhari ya taka wajen samar da zaman lafiya a Afrika
Nouackcott - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya samu lambar yabo daga wajen kungiyar zaman lafiya ta Abu Dhabi bisa rawar da ya taka wajen wanzar da zaman lafiya a Afrika.
An gabatarwa shugaba Buhari wannan kyauta ne ranar Talata a birnin Noukchott, kasar Larabawan Mauritania.
An kafa kungiyar AbuDhabi Peace Forum ne a shekarar 2015 a kasar UAE domin karfafa da'awar addinin Musulunci wajen samar da zaman lafiya da iya mu'amala tsakanin addinai mabanbanta.
Wadanda ke hallare a taron sun hada da shugaban kasar Mauritanai, Mohamed Ghazouani; Shugaban Abu Dhabi Peace Forum da Al Mahfoudh Bin Bayyah, Sakataren kungiyar.
Kalli hotunan taron:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng