Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matar Ma'aikacin Kamfanin NNPP a Osogbo
- Wasu da ba'a gano ko su waye ba sun je har gida sun sace wata yar kimanin shekara 51, Oluwatoyin Ojo a Osogbo, jihar Osun
- Wasu rahotanni daga yankin sun ce wacce aka sace matar wani ma'aikacin NNPC ce kuma lamarin ya faru a daren Jumu'a
- Kwamandan dakarun Amotekun ya tabbatar da cewa zasu ceto matar kuma su damke masu garkuwan
Osun - Wasu mutane da ba'a san ko su waye ba sun yi garkuwa da wata mata yar kimanin shekara 51, Oluwatoyin Ojo, a Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Wata majiya daga cikin iyalan matar, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo yace Mijin Misis Ojo ma'aikacin NNPC ne a Defot din Warri.
Majiyar ta bayyana cewan an yi awon gaba da Ojo ranar Jumu'a da misalin karfe 10:30 na dare a gidanta da ke Layin Landero, kusa da kwalejin fasaha a Osogbo.
Wakilin jaridar Premium times bai yi nasarar gano ko maharan sun tuntubi iyalan matar domin neman kuɗin fansa ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma mazaunin Anguwar da lamarin ya faru ya ce:
"Ban da tabbacin ko masu garkuwan sun kira iyalan matar domin neman kuɗin fansa saboda bamu ji labarin hakan ba tun da aka sace ta."
Fargaba da tsoro sun mamaye zukatan mazauna yankin yayin da suka fara kira ga jami'an 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro su kawo masu ɗauki.
Wane mataki jami'an tsaro suka dauka?
Kwamandan dakarun Amotekun, Amitolu Shittu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni dakarunsa suka fara farautar makwamusan domin ceto matar cikin koshin lafiya.
Jaridar Punch ta ce kwamandan Amotekun ya tabbatar da cewa wacce aka sace matar wani ma'aikacin kamfanin Man Fetur na kasa NNPP ce wanda ke aiki a Defot na Warri.
Mista Shitu yace mijin matar, Festus Ojo, ya kira shi ta wayar salula domin gaya masa cewa an yi garkuwa da mai dakinsa.
Shugaban Amotekun ya tabbatar da cewa dakarunsu zasu cafke masu garkuwan kuma su ceto matar lami lafiya.
Gwamnati ta sa dokar zaman gida a Neja
A wani labarin kuma Matasa Sun Halaka Basarake Har Gida, Gwamnati Ta Kakaba Dokar Kulle a Neja
Rikici tsakanin matasa ya yi ajalin magajin garin Lambata, yankin Gurara a jihar Neja, Mohammed Abdulsafur, bayan sun shiga gidansa.
Gwamnatin jihar Neja ta sanya dakar zama gida daga 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe har sai baba ta gani, ta yi Allah wadai da kisan.
Asali: Legit.ng