Jihohi 8 Da Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Cikin Kwanaki 30
- Shugaba Muhammadu Buhari zai taya Asiwaju Bola Tinubu kamfen a jihohi takwas cikin kwanaki 30
- Bashir Ahmad, hadimin shugaban Buhari kan kafafen yada labaran zamani, ya bayyana hakan
- A cewar Ahmad, APC ta yi kamfen a wasu jihohi biyu gabanin yanzu amma duk da haka zasu koma
An shirya Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihohi takwas tsakanin ranar 23 ga Junairu da 21 ga Febrairu don kamfen shugaban kasa wa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Bashir Ahmad, hadimin shugaban Buhari kan kafafen yada labaran zamani, ya bayyana shirin tafiyar da shugaban kasan yayi na kamfen a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 14 ga Junairu.
Ahmad ya cewa wannan sabon sauyi ne a yakin neman shugaban kasa na APC da jam'iyyar tayi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jawabin da ya fitar, yace:
"Sabon Sauyi: Yakin neman zaben shugabancin kasan Tinubu/Shettima da shugaba Buhari zai halarta"
Ga jerin jihohin da Buhari zai halarta:
23/01/23 = Bauchi
30/01/23 = Akwa Ibom
04/02/23 = Nasarawa
06/02/23 = Katsina
09/02/23 = Sokoto
14/02/23 = Imo
16/02/23 = Kano II
21/02/23 = Lagos II Na Karshe
A jerin dake sama, jihohi biyu cikin wadanda shugaba Buhari zai kai ziyara na karkashin ikon jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) yayinda sauran shidan na APC ne.
Hakazalika an nuna cewa APC za ta gudanar da sabon kamfen bayan wanda tayi a baya a jihohin Kano da Legas.
Kano da Legas ne jihohi mafi adadin kuri'u a bisa alkaluman da hukumar zabe ta INEC ta fitar.
Na yi iyakan kokari na kuma ku shaida ne, Buhari Ga Al'ummar Yobe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ziyarar kaddamar da ayyuka da kamfen da ya kai jihar Yobe ya bayyanawa mabiyar jam'iyyar APC cewa ya yi iyakan kokarinsa kuma al'ummar jihar shaidu.
Buhari ya ce gabanin hawansa mulki, rikicin Boko Haram ya addabi al'ummar Arewa maso gabashin Najeriya.
An gudanar taron yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC a Damaturu ranar Talata, 10 ga Junairu, 2023.
Buhari ya bada labarin yadda ya dade yana neman mulki amma bai samu ba.
Asali: Legit.ng