An Sallami Farfesa Daga Jami'a a Amurka Bayan Kai Kararta Ta Nunawa Dalibai Hoton Annabi

An Sallami Farfesa Daga Jami'a a Amurka Bayan Kai Kararta Ta Nunawa Dalibai Hoton Annabi

  • Wata Farfesa ta rasa aikinta a Amurka kan nunawa daliban ajinta zanen hoto da sunan Annabi Muhammadu (SAW)
  • Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Amurka sun caccaki jami'ar bisa korar Malamar saboda wannan dalili
  • Shugabannin Jami'ar sun bayyana cewa ta yanke shawara korar Farfesar ne saboda hakan shine mafi alkhairi garesu

Wata jami'a mai zaman kanta dake St. Paul, Minnesota Amurka, Hamline University, ta sallami wata Malamar makarantar, Farfesa Erika López Prater kan nunawa daliban zanen hoto cewa na Annabi Muhammadu (SAW) ne.

An sallami Farfesar ne bayan wata daliba cikin daliban makarantar ta shigar da kararta wajen hukumar jami'ar.

Farfesa Erika López Prater masaniyar tarihi ce mai karantar da dalibai ilmin tarihi.

New York Times ta ruwaito cewa Shugabar jami'ar, Fayneese Miller, ta sallama farfesar bisa rashin girmama ra'ayin dalibai Musulmi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babbar Kotu Ta Kori Sanatan APC Daga Takara a Zaben 2023

Musulmai a fadin duniya basu amince da zanen Annabinsu ba kuma suna ganin yin haka batanci ne.

Hamline
An Sallami Farfesa Daga Jami'a a Amurka Bayan Kai Kararta Ta Nunawa Dalibai Hoton Annabi Hoto: @saharareporters
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

DailyMail ta ruwaito cewa a ranar 6 ga Oktoba, 2022, farfesar ta daura hotunan yayin karatu da dalibai ta yanar gizo.

Hakan ya tada hankulan daliban dake halarce musamman Aram Wedatalla, shugabar dalibai Musulmai na jami'ar.

Kai tsaye ta shigar da kara wajen hukumar jami'ar.

Jaridar daliban jami'ar, The Oracle, a ranar 6 ga Disamba ta bada rahoton bidiyon farfesar lokacin da farfesar ta fadi hakan.

Bidiyon ya nuna cewa gabanin nunawa dalibai hotunan, ta bukaci Musulmai su fita daga ajin idan sun san basu son ganin hotunan.

Yaushe aka sallameta

Wata Farfesar Addinin Musulunci a jami'ar Michigan, Christiane Gruber, ce ta fara bayyana labarin sallamar Farfesa Erika a mujallar New Lines Magazine.

Kara karanta wannan

Adamawa Ta Cika Ta Batse Yayin da Shugaba Buhari Ya isa Mahaifar Atiku Don Yakin Neman Zaben APC

Gruber ta ruwaito daya daga cikin mataimakan shugaban jami'ar, David Everett, da cewa:

"An yanke shawara kan cewa zai fi zama alkhairi ga jami'ar Hamline a sallami Malamar."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida