Kai Tsaye: Yadda Kamfen Shugaban Kasa Ke Gudana Yau a Damaturu

Kai Tsaye: Yadda Kamfen Shugaban Kasa Ke Gudana Yau a Damaturu

Ba tare dabata lokaci ba daga jihar Adamawa, Jirgin shugaba Muhammadu Buhari tare da manyan jiga-jigai kuma mambobin kwamitin yakin neman kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress APC ya garzaya jihar Yobe.

Shugaba Muhammadu Buhari, tare da dimbin hadimansa zasu tafi kaddamar da kanfen Tinubu a jihar tare da neman zarcewa Mai Mala Buni.

Ku yi noma, Buhari ya yi kira ga al'ummar Yobe

Shugaba Buhari yace:

"Ba abinda zan fadi da ba'a fadi ba. Abinda ya kawo ni nan Yobe daga Adamawa shine jam'iyyarmu ta APC ta yarda da cewa Ahmed Bola Tinubu shine wanda jam'iyya ta tsaida ... saboda haka abinda ya kawo ni kenan."
"Tun da karfe 12 ko kafin lokacin kuke cikin rana kuka saurari yadda muka samu kasa shekara bakwai da suka wuce."
"Kun fi kowa sanin cin mutuncin da Boko haram sukayi muku, suka kona makarantu, suka hana yaranku karatu, saboda haka Allah ya taimakemu mun ga bayansu."
"Ina son ku maida hankali idan Allah ya kawo damina ku noma abinda zaku ci. Idan damina ta wuce ku smau sana'ar da zaku yi."
"Ni na tashi maraya, ban san mahaifi na ba. Kuyi iyakan kokarinku ku biya amanar da aka baku da ta iyalin ku."
"Abin duniya abin banza, ku rike amana, ku rike jama'ar da ke karkashin ku."
"Na shekara 80, na yi aikin soja, na yi na ofis, na shiga siyasa, na nemi shugaban kasa sau uku, na shiga shari'a na ce a tausaya min, sai aka min dariya"
"Dan Allah ku zabi wanda kuke so. Ku kun sani iyakan kokarin da mukayi. Zamu cigaba da aiyukan kokarinmu, Zamu tabbatar da cewa an zanna lafiya, ya kiyayemu daga dukkan sharri."
"Mu mun gama namu Insha'aLLahu, nan da wata biyar zamu koma gida."

Kada ku bari a yaudareku, zan muku aiki tukuru: Tinubu

Wakilin jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi dogon jawabi inda yayi kira ga yan Najeriya kada su yarda jam'iyyar PDP ta yaudaresu.

Tinubu ya yi alkawarin cewa zai yiwa yan Najeriya ba dare ba rana idan ya samu nasara.

Asiwaju Tinubu ya ce wannan karan ba wasa suka zo yi ba, aiki tukuru zasu yi idan suka hau mulki.

Borno da Yobe kamar Hassan da Husaini ne: Shettima ya fadi da Kanuri

Dan takaran kujerar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, yana gabatar da nasa jawabin a yaren Kanuri.

A dan ballin da muka fahimta, ya ce lokacin PDP jihar Borno da Yobe ta sha fitinar Boko Haram zamanin PDP amma yanzu abubuwa sun yi sauki.

Yace:

"Borno da Yobe kamar Hassan da Husaini ne."

PDP mayaudara ne, sun cuci Najeriya, Buhari kai ne ka gyara kasar nan: Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, a jawabinsa ya fara da caccakar jam'iyyar adawa ta PDP.

Lawan yace ya kamata PDP taji kunyan yawon kamfen a kasar saboda irin lalata kasar nan da suka yi.

"Zamu yi zabi jam'iyyarmu ta APC a duka jihohin APC. Kada wani yaudare mu, a ce wani yana takara daga wannan yanki, sun yi takara a baya amma basu yi mana kowa ba, hasali ma sharri suka yi mana."
"Ba ma zaben wani don dan wannan yankin ne. Babu wani zaben tumun daren da za'ayi."

Mutane na da saurin mantuwa, sun manta yadda Buhari ya sami kasar nan - Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Atiku Bagudu, a jawabinsa ya mika godiya ga shugaba Buhari bisa namijin kokarin da yayi wajen gyara Najeriya.

Bagudu ya ce yan Najeriya na da saurin mantuwa, sun manta yadda aka samu kasar nan cikin rashin tsaro da rashin kudin biyan albashin ma'aikata amma Buhari ya kawar da wadannan matsaloli.

Ya ce:

"Buhari muna maka godiya bisa halartan wannan taro bayan kaddamar da wasu ayyuka jiya a Yobe."

Bagudu
Kai Tsaye: Yadda Kamfen Shugaban Kasa Ke Gudana Yau a Damaturu
Asali: Twitter

Baba Buhari ya fidda mu yan Arewa daga kunya, Lalong

Gwamnan jihar Plateau kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan jam'iyyar APC, Simon Lalong, ya bayyanawa daukacin mabiyan APC cewa Shugaba Buhari ya fidda yan Arewa daga kunya.

Lalong ya ce Buhari ya samar da arzikin man fetur a jihar Bauchi amma Atiku na son sayarwa wadannan rijiyoyin na man.

Ya yi kira da yan jihar Yobe su zabi Asiwaju Bola Tinubu.

Shugaba Buhari ya dira filin kamfen a Damaturu

Shugaba Buhari ya dira filin taron yakin neman zaben dake gudana yanzu haka a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Buhari ya Damaturu, jihar Yobe

Shugaba Buhari ya dira birnin Damaturu, misalin bayan Azahar domin kaddamar da kamfen.

Hadiminsana soshiyar midiya, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan a Tuwita.

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida