Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu a Kan Kasafin Kudin 2023
- Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kudin shekarar 2023 a yau Talata, 3 ga watan Janairu
- Buhari ya saka hannu a kasafin kudin da jimillarsa ya kai naira tiriliyan 21.83 a wani dan buki da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Wannan shi ne kasafin kudi na takwas kuma na karshe da gwamnatin Buhari ta sanyawa hannu a matsayin shugaban kasa
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin 2023 a ranar Talata, 3 ga watan Janairu.
Tun farko majalisar dokokin kasar ta aiwatar da kasafin kudin da ya kai jimillar naira tiriliyan 21.83.
Shugaban kasar ya rattaba hannu a takardar a fadar shugaban kasa a gaban shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan; Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran mambobin majalisar dokokin tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa kakakin shugaban kasa Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya saki.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata a Abuja ya sanya hannu a kan kasafin kudin 2023 na naira tiriliyan 21.83 tare da karin kasafin kudin 2022.
“Da yake jawabi a wajen sanya hannu a kasafin kudi na takwas kuma na karshe a wannan gwamnai, shugaban kasar ya ce jimillar kudaden da za a kashe ya kama naira tiriliyan 21.83, Karin naira tiriliyan 1.32 kan kasafin kudin baya na naira tiriliyan 20.51."
Buhari ya baiwa ministar kudi aikin haduwa da majalisar dokoki don yin gyare-gyare a wuraren da ya kamata
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kasar ya ce ya saka hannu kan kasafin kudin ne domin bayar da damar fara aiwatar da shi ba tare da bata lokaci ba.
Ya umurci ministar kud, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Hajiya Zainab Ahmed, da ta hadu da majalisar dokokin kasar don yin gyare-gyare a inda ya kamata a kasafin kudin.
A wani labari na daban, shugaban kasa Buhari ya ba da lamarin yadda rayuwarsa ta kasance a lokacin da yake matashi a makaranta.
Buhari ya ce ya sha bulala sosai a hannun malamai saboda sam baya son zuwa gonar makarantarsu a lokacin damina.
Asali: Legit.ng