Hutun Da Za a Yi a Najeriya a 2023: Bikin Sallah, Easter da sauran Hutun Da Ya Kamata Ku Sani
Domin bikin sabuwar shekarar 2023 da ya fara a yau, Lahadi, 1 ga watan Janairu, yan Najeriya za su yi hutun aiki a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu kamar yadda gwamnatin tarayya ta ayyana.
Hutun sabuwar shekarar guda daya ne a cikin hutu 16 da yan Najeriya za su mora a shekarar 2023.
Idan gwamnatin tarayya ta ma'aikatar cikin gida ta ayyana hutu, hakan na nufin makarantu, kasuwanci, bankuna da ofishoshin gwamnati za su zama a rufe a wannan rana.

Source: Getty Images
Don haka, sanin ranakun hutun zai taimakawa mutum wajen tsara shirye-shiryensa da kyau.
Hutun Najeriya a 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin hutun aiki da za a sha a 2023.
- Lahadi 1 ga watan Janairu - Ranar sabuwar shekara
- Litinin, 2 ga watan Janairu - Ranar Hutun sabuwar shekara (gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin ranar hutu saboda ranar sabuwar shekara ta fada Lahadi)
- Juma'a, 7 ga watan Afrilu - Hutun 'Good Friday'
- Litinin 10 ga watan Afrilu - Hutun Easter
- Asabar, 22 ga watan Afrilu - Bikin karamar Sallah
- Litinin, 24 ga watan Afrilu- Eid-el Filtri
- Litinin, 1 ga watan Mayu - Ranar ma'aikata
- Asabar, 27 ga watan Mayu - Ranar yara (Hutun makarantun gwamnati da yara kawai)
- Litinin, 12 ga watan Yuni - Ranar Dimokradiyya
- Alhamis, 29 ga watan Yuni - Babban sallah
- Juma'a, 30 ga watan Yuni - Eid el Kabir
- Asabar 27 ga watan Satumba- Hutun Maulidi
- Lahadi, 1 ga watan Oktoba - Ranar yancin kai
- Litinin, 2 ga watan Oktoba - Hutun ranar yancin kai saboda ya fada a Lahadi
- Litinin, 25 ga watan Kirsime - Ranar Kirsimeti
- Talata, 26 ga watan Disamba - Ranar 'Boxing Day'
Za mu kawowa Atiku kuri'u miliyan 1 a 2023, kungiyar yan Najeriya mazauna Turai
A wani labarin, Wata kungiyar yan Najeriya mazauna Turai ta bayyana cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya cancanci jan ragamar kasar nan a 2023.
Kungiyar wacce ta yi alkawarin kawowa Atiku kuri'u miliyan daya ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar na da gogewa a shugabanci ta yadda zai bunkasa tattalin arzikin kasar kamar yadda take muradi.
Don cimma wannan kudiri nata, kungiyar ta nada jagorori a fadin kasashen Turai.
Asali: Legit.ng
