2022: Hisbah Ta Cafke Wadanda Ake Zargi 2,260, Ta Kwashe Almajirai 1,269
- Hukumar daidaita sahu ta jihar Kano a karkashin jagorancin Sheikh Harun Ibn Sina, ta sanar da kama mutum 2,260 da take zargi da aikata laifuka daban-daban a Kano
- Sheikh Sina ya sanar da cewa, sun tarwatsa motoci 25 dauke da kwalabe dubbai na giya a jihar duk a cikin wadanda ta kama a fadin jihar Kano
- Hukumar tayi nasarar kwashe almajirai 1,269 daga kananan hukumomi takwas na kwaryar birnin Kano inda tayi nasarar mayar da wasu garuruwansu
Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano tace tayi nasarar kama wadanda ake zargi 2,260 kan aikata laifuka daban-daban a sintirin ta daga Janairu zuwa Disamban 2022.
Hakazalika, jimillar mabarata 1,269 ta kwashe daga kan tituna a kananan hukumomi takwas na kwaryar birnin Kano wanda 386 daga ciki aka mayar dasu jihohinsu matsayin kokarin hana bara a fadin jihar.
Kuturu da Kudinsa: EFCC Ta Kada Kararrawa Kan Wasu Kadarori, Tana Gayyatar 'Yan Najeriya Masu Sulalla
Kwamandan hukumar, Sheikh Harun Sina, ya bayyana hakan yayin jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis.
Kamar yadda yace, da yawa daga cikin wadanda aka kama kan laifuka daban-daban an mika su ga hukumomin tsaro don daukar matakan da suka dace yayin da masu karancin shekaru aka mika su ga iyalansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamandan yayi bayanin cewa, a bangaren magance matsalolin al’umma, hukumar tayi nasarar tarwatsa tarukan rashin da’a 86 da suka hada da auren jinsi, casun ‘yan kwaya da sauran matsaloli a fadin jihar, jaridar Punch ta rahoto.
Sina yayi bayanin cewa, hukumar ta sasanta rikici 822 yayin da wasu yanzu suke hannun kuliya saboda yanayin matsalolin dake kunshe.
“Hukumar ta aurar da mutane 15 yayin da ta Musuluntar da 22 yayin Da’awah a 2022.”
- Yace.
Ya bayyana cewa, motocin giya 25 dake dauke da dubban kwalaben giya suka tarwatsa a 2022 inda suka ce za a tarwatsa wasu kari a watan Janairun 2023, jaridar The Guardian ta rahoto.
Gwamnatin Kano tana Kokari
A bangaren karfafa lamurran Hisbah, Sina yace gwamnatin jihar Kano ta dauka jami’ai manya 5,700 aiki a hukumar tar EFCC da kanana 3,100 bayan karin sabbin gine-gine tare da gyara hedkwatocin hukumar da tayi.
Yace jami’an Hisbah 1,000 aka horar a sansanin masu hidimtawa kasa sake Kusalla a karamar hukumar Karaye ta jihar inda ya kara da cewa gwamnatin ta samar musu da sabbin inifam tare da sauran kayan aiki don karfafa musu guiwa.
Kwamandan ya bayyana cewa an kafa sabuwar kotun Shari’a a hedkwatar Hisbah dake Sharada Kano yayin da Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya amince da karawa Masallacin Hisbah matsayi zuwa na Juma’a.
Yace an dauka nauyin jami’an Hisbah shida zuwa Saudi Arabia yayin aikin Hajji don taimakawa mahajjatan Kano.
Ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su bude ido tare da kai rahoton duk wasu jama’ar da ake zargi ko dabi’a da bata dace ba ga hukumomin da suka dace yayin da hukumar ba zata yi kasa a guiwa ba wurin tsarkake jihar daga dukkan laifuka ba.
Budurwa ta fada son boka, ta bayyana bidiyonsu
A wani labari na daban, wata budurwa kyakyawa ta fada soyayyar wani boka.
Bidiyonsu ya bayyana suna tsakar kogi sun zuba soyayya cike da shauki da kaunar juna.
Asali: Legit.ng