Gwanjo: EFCC na Gayyatar 'Yan Najeriya su zo su Siya Kadarorin da ta Kwace Daga Mahandama

Gwanjo: EFCC na Gayyatar 'Yan Najeriya su zo su Siya Kadarorin da ta Kwace Daga Mahandama

  • Hukumar EFCC ta kadawa wasu kadarorin da suka kwato daga mahandama kararrawa kuma tana gayyatar 'yan Najeriya da su garzayo
  • Hukumar ta bayyana cewa, za a fara gwanjon kadarorin ne daga ranar Litinin, 9 ga watan Janairu kuma kofa bude take ga duk mai sulalla
  • Ta sanar da cewa, kadarorin an kwato su ne daga mahandama kuma kwacewar dindindin bayan hukuncin kotu

FCT, Abuja - Hukumar da ke yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta bayyana shirin yin gwanjon wasu kadarorin da gwamnatin tarayya ta kwace daga mahandama.

An yi nasarar kwace kadarorin ne bisa umarnin kotu da EFCC ta samu tsawon shekaru.

Hukumar EFCC
Gwanjo: EFCC na Gayyatar 'Yan Najeriya su zo su Siya Kadarorin da ta Kwace Daga Mahandama. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce a ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar ta sanar da fara gudanar da gwanjon tare da yin talla a wasu manyan jaridu na kasar nan don gayyatar masu bukatar siya.

Kara karanta wannan

Shahararren Dan Takarar Gwamnan APC Ya Dage Kamfen Dinsa, Ya Bada Dalili

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, hukumar ta kara da bukatar mahalarta ko kungiyoyi masu sha’awar siyan dad su gabatar da bukatarsu tun daga ranar Litinin, 9 ga Janairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta ce za a gudanar da gwanjon ne bisa ga dokar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na shekarar 2004.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya sanar a ranar 16 ga watan Disamba cewa, nan ba da jimawa ba hukumar za ta fara sayar da kadarorin da aka yi watsi da su a fadin kasar nan bayan kammala siyar da motocin da aka yi watsi da su a fadin kasar.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kamala gwanjon motocin da aka kwace a fadin kasar. A daya daga cikin gwanjon da aka yi a Abuja, Premium Times ta lura da yadda tsarin ke nuna rashin gaskiya.

Kara karanta wannan

Abin nema: Majalisa ta amince da bukatar Buhari, zai sake runtumo bashi mai yawa

Bawa ya bayyana adadin dukiyar da suka samu daga tsohon akanta janar

A wani labari na daban, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC ya sanar da adadin dukiyar da suka samo daga Idris Ahmed.

Bawa ya sanar da cewa, sun karbo kudin da ya kai adadin N30 biliyan daga hannun tsohon akanta janar na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng