CBN Ya Kashe N800bn Wajen Buga Sabbin Naira Da Lalata Tsaffi

CBN Ya Kashe N800bn Wajen Buga Sabbin Naira Da Lalata Tsaffi

  • Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana makudan kudin da yake kashewa wajen buga sabbin kudi da lalata tsaffi
  • A watan nan na Disamba, gwamnatin tarayya ta fitar da sabbin takardun Naira tare da lalata tsaffi
  • Rikici ya mamaye babban bankin CBN kan maganar kudin 'Stamp Duty' da Gudaji kazaure ya fallasa

Abuja - Mataimakiyar gwamnan CBN, Aisha Ahmed, ta bayyana cewa kudin da ake kashewa kan buga sabbin kudi a shekara ya karu da N10bn.

Aisha ta bayyana hakan ne ranar Juma'a yayinda da gurfana gaban majalisar wakilan tarayya a madadin gwamnan bankin, Godwin Emefiele.

Ta bayyana cewa kashi 90% na kudin da take kashewa kan manajin Naira buga sabbin takardun kudi ake da su.

Punch ta ruwaito cewa babban bankin na kashe N150bn wajen buga sabbin kudi da lalata tsaffi a shekara.

Kara karanta wannan

An Suburbudi Wani Mutumin Da Yaje Sayen Abinci Da Sabon Naira, Bidiyo

Hakazalika tsohon mataimakin gwamnan CBN, Dr Kingsley Moghalu, shima ya ce lallai ana kashe kimanin N150bn a shekara.

Ya ce ana amfani da kudin ne wajen buga sabbi, ajiyansu, tafiyar da su, kare su da kuma lalata tsaffi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

CBN Gov
CBN Ya Kashe N800bn Wajen Buga Sabbin Naira Da Lalata Tsaffi
Asali: Getty Images

Bisa jawabin Aisha Ahmed, bankin ta kashe N800bn tsakanin 2017 da 2021 wajen kula da Naira.

Tace:

"An yi binciken cewa kudin da aka kashe wajen kula da Naira daga 2017 zuwa 2021 ya karu da N10bn a shekara kuma kashi 90% na wannan kudi buga sabbin takardun Naira ake da su."
"Wannan na illata ayyukan CBN."

Aisha Ahmad ta ce daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta shine yadda ake buga jabun takardun Naira a jihohi, har da birnin tarayya Abuja.

Ta kara da cewa hakan na illata yan kasuwa da kuma tattalin arzikin kasan ga baki daya.

Kara karanta wannan

Buhari ya fadi kudaden da ya kashe wajen gyara ofisoshin 'yan sanda da bariki a cikin shekaru 3

Saura kiris a yiwa wani mutumi zindir a gidan abinci kan sabon kudin Naira

Wata mata mai sayar da abinci ta kusa yiwa wani dan Najeriya tumbur a gidan abinci yayinda yayi kokarin biyanta da sabuwar takardar Naira N1000 da babban bankin Najeriya CBN ya buga.

Matar ta bayyana cewa ita dai bata taba ganin kudin ba kuma mutumin damfararta yake son yi.

A bidiyon da ya yadu da Instablog ya wallafa Tuwita ranar Juma'a, matar ta rike masa wando har sai da ya yage.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida