Manyan 'Barayi' da 'Macuta' Al'umma 4 Da Asirinsu Ya Tonu a 2022

Manyan 'Barayi' da 'Macuta' Al'umma 4 Da Asirinsu Ya Tonu a 2022

Shekarar nan 2022 ta zo karshe inda ana saura kasa da mako guda da karewarta.

A wannan shekara, jami'an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC ta samu gagarumin nasarar bankado barayin kudin gwamnati.

Hakazalika hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta yi babban kamu na babban jami'in dan sanda.

A cewar DailyTrust, wadannan hudun ne manyan barayin da aka fi tattaunawa kan lamuransu a 2022.

1. Abbas Ramon Hushpuppi

Dubun mayaudari kuma madamfari, Abbas Ramon Hushpuppi, ya cika bayan shekara da shekaru yana kwashe kudaden mutane ta yanar gizo.

Gwamnatin kasar Dubai ta damkeshi a kasarta kuma ta mayar da shi kasar Amurka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan watanni ana hukunci, kotu ta yanke masa hukuncin watanni 135 a gidan gyari hali.

Kara karanta wannan

Saura kwanaki 20: Gwamnatin Kano ta aiwatar da umurnin kotu kan Abduljabbar, saura na kisa

Bayan haka a umurcesa ya biya mutum biyu cikin wadannan ya yaudara $1,732,841 (£1,516,182)

2, Abba Kyari

A Maris 2022, hukumar hana amfani da muggan kwayoyi NDLEA ta kama dakataccen DCP, Abba Kyari, bisa laifin safarar hodar iblis.

An gurfanar da Abba Kyari tare da wasu yan sanda 6 da suka aikata laifin tare.

Sun hada da ACP Sunday J. Ubia, ASP Bawa James, Insp. Simon Agirigba da Insp. John Nuhu.

An kama Abba Kyari hannu dumu-dumu a faifan bidiyo yana bayanin yadda za'a karkatar da hodar iblis.

Hakan ya biyo bayan samun hannunsa cikin harkokin Hushpuppi.

Ahmed Idris
Manyan 'Barayi' da 'Macuta' Al'umma 4 Da Asirinsu Ya Tonu a 2022
Asali: Twitter

3. Ahmed Idris

A Yuli 2022, wata babban kotun tarayya dake zaman a Abuja ta bada umurnin garkame tsohon Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris, bisa karkatar da kudi N109bn.

EFCC ta ce Ahmed Idris da wadanda suka aikata laifin tare da shi sun gurfana gaban kotu kan laifuka 14 na sata da almundahana.

Kara karanta wannan

Buhari ya fadi kudaden da ya kashe wajen gyara ofisoshin 'yan sanda da bariki a cikin shekaru 3

Sauran sun hada da Godfrey Olusegun Akindele, Mohammed Kudu Usman, da kasuwar Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

Kai tsaye Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta dakatar da shi, Daga bisani hukumar EFCC ta ce ta kwato makudan kudade N30bn daga hannunsa.

4. Eno Ubi Otu

A Agusta 2022, hukumar EFCC ta damke Diraktan kudi na hukumar raya yankin Neja Delta NDDC, Mr. Eno Ubi Otu, bisa almundahanar N25bn.

An damke Otu ne cikin binciken babakeren da ake gudanarwa kan NDDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida