Bautar Kasa Wajibi Ne Ga Matasan Da Suka Kammala Karatu Kuma Ba Za'a Fasa Yinsa Ba, Minista

Bautar Kasa Wajibi Ne Ga Matasan Da Suka Kammala Karatu Kuma Ba Za'a Fasa Yinsa Ba, Minista

  • Ministan wasanni na cewa babu wani kudiri na ganin an canja tsarin hukumar NYSC na maida shi zabi ga daliban da suka kammala makaranta
  • Tsarin dai hukumar NYSC shi ne, duk wanda ya kammala makaranta a matakin digiri ko babbar Diploma
  • An fara shirin ne tun mulkin tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Yakubu Gowon

Abuja: Ministan ma'aikatar wasanni da matasa, Mr. Sunday Dare, yace babu wani dalilin da zai sa ace an maida tsarin bautar kasa zabi ga wanda suke yi.

Ministan yace hakan ne a lokacin da ma'aikatar take bikinta a karo na biyu na bayyana aikin shugaba Buhari da nasarorinsa daga 2015-2023 a ranar talata.

Yace dalilin kirkirar hukumar NYSC, a shekarar 1973, shi ne dan bunkasa hadin kai da zamantakewa a tsakanin al'umma.

Kara karanta wannan

Yadda Al'umma Suka Hadu Suke Gasar Cin Abinci a Jihar Cross - RIver

NYSC.
Da Walakin: Bamu Da Burin Mu Maida NYSC Ya Zama Sai Kai Niyya Minista Dare Hoto: NYSC
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dare yace rayuwarsu shi ne yadda za'a bunkasa yadda za'a inganta rayukan matasa da sa musu kishi.

"Dalilin kirkirar wannan tsarin wanda Janar Yakubu Gowon ya kirkira a Nigeria shine dan ganin hadin kan Nigeria ya dore"

Yace kwannan za'a kafa kwamitin da zai shirya bikin hukumar ko tsarin cika shekara 50 da kafuwa. kamar yadda PMNews ta rawaito

Ya naya karawa cewa:

"Babu wani dama da za'a ce mutum ya ce zai zaba ace yayi ko kar yayi tsarin, a'a wannan zance ne"

Za'a Bunkasa Tsarin NYSC

Ya ce suna nan suna suna fitar da tsarin da zai kara inganta hukumar da aiyukanta.

yace zasu bude wani tsari da zasu gyara yadda hukumar take ajiye bayanai, zaku ma su gyara yadda ake tsarin tabbatar da sahihancin sakamakon dali bai musamman wanda suka fito daga jami'oi.

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

Ireports ta rawaito cewa tun da ga cire tsohon shugaban hukumar Janar Muhammad Kuku Fada, zaku fahimci cewa anayi ne dan ku (matasa).

Yace shugaba buhari bazai hukumar ta lalace ba sabida sakaci ko kuma rashin iya gudanar da aiki. An cire dai tsohon shugaban hukumar Muhammad Kuku Fada a watan Nuwanban wannan shekarar, wata shida bayan hawansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel