Gaske: Yadda Akai Gasar Saurin Cin Abinci A JIhar Cross River

Gaske: Yadda Akai Gasar Saurin Cin Abinci A JIhar Cross River

  • Wani bidiyo ne da editan jaridar The Union ya wallafa a shafinsa yake nuna yadda wasu mutane suka hadu a bakin titi suke gabzar Fufu.
  • A bidiyon ana iya gani kowanne mai gasar zaune da Fufu a gabansa, kusa da shi kuma akwai dan tayi
  • Ana jin an kunna musu kida a bidiyon yayin da suke ta fafatwa, a tsakaninsu, ko in sun gama za'a nada sarkin cin abinci?

Cross- River: Wani bidiyo ne da ya yadu aka kafafen sadarwa na zamani kan yadda wasu mutane ke bikin al'adar cin fufu.

Rukunin mutanen sun taro ne a Ogojo dake jihar Rivers, suna gudanar da bikinsu na cin abinci da sukeyi duk shekara.

Bikin wanda ake yinsa duk shekara, wanda yake nuna irin amfanin gonar da aka samu, kuma ana yi ne sabida wata al'ada ce da ake son kar ta mutu a rayata.

Kara karanta wannan

Rikici Kan Bazawarar Yan Bindiga Ya Janyowa Mutane Asarar Rayukan Mutum 69 a Zanfara

Garuruwa da dama a Nigeria na gudanar da irin wannan bukukuwan, musamman ma garuruwan da suke samar da wani nau'i na abinci.

Kamar a jihar Niger, da wani bangare na makociyarta kogi, suna bikin dukan sakwara wadda ake samarwa da ga doya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abinci
Gaske: Yadda Akai Gasar Saurin Cin Abinci A JIhar Cross River
Asali: Twitter

Wannan gasar dai anyi ta ne a Ogoja zuwa Iyala dake jihar Cross River. A bidiyon anga yadda mutane su taru suke kallon bikin.

A bidiyon anga wani wani mutum zaune a gaban tulin Fufu wanda aka sarrafashi da doya rogo na zaune na dibansa yayin da taron mjutane ke shewa da sowa.

kalli bidiyon a kasa:

Mutane Da Yawa Sunci Abinci Sun Mutu

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu a karamar hukumar Abi ta jihar Cross River bayan cin abinci mai guba.

Kara karanta wannan

Aure a Kudancin Koriya: Al'adr Daure Kafafun Ango Ana Zugarsa da Bulala Cike da Nishadi

Sakataren dindindin na ma'aikatar lafiya ta jihar Cross River, Dr Iwara ya tabbatr da faruwar lamarin ga kafar labarai ta Channels Tv a ranar Asabar 17 ga watan Disamaba.

Ya bayyana cewa jami'an taimakon gaggawa ciki harda Red Cross dana hukumar yaki da annoba da ma'aikatar lafiya sun tafi da mutane da abinda ya shafa don min bincike sosai a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: