Amfanin Da ke Tattare Da Yin Kuka Bincike Daga Masana Harkar

Amfanin Da ke Tattare Da Yin Kuka Bincike Daga Masana Harkar

  • Kuka wata halayyace da mutum ke nuna yadda wani abu ya sameshi daga farin-ciki, bakin-ciki, damuwa, amma shin hakan yana da amfani?
  • Ba haka kurum yake kuka ba, daga cikin mata ko maza kowa na kuka, a kasar Amurka, mata sun fi maza yin kuka da kashi 3.3.
  • Amma wani abu da musane basu sani ba shine yadda dabbobi ke yin kuka, a wani bincike da wasu masa na sukai sun gano amfaniyin kukan.

Me yasa mutane ke yin kuka?

Bincike: Mutane nayin kuka kala uku kamar yadda bincike ya nuna.

Fitar da hawaye sosai: akwai kukan da mutane sukeyi sosai wanda suke fitar hawayen su kan kwaranya ba tare da tsinkewa ba.

Fitar da hawaye na lokaci daya: akwai hawayen da mutane suke yinsa a loakaci daya ba tare da ci gaba da kwaranyarsa ba. irin wannan hawayen na faruwa ne idan mutum yaji rauni, ko aka bugeshi ko kuma ya kware.

Kara karanta wannan

“Fatan Zai Saka”: Hamshakin Mai Kudi ya Siya Gwanjon Wando Mai shekaru 165 kan N50m

Zubar hawaye a kunci daya: mutane kan zubar da hawaye a kunci daya, ko kuma a kowanne kuncin a loaci daban-daban musamman lokacin da suka samu wani shauki na murna ko akasin haka.

yawanci in mutane sunyi magana akan suna yinta ne akan kukan damuwa ko kuma na wani abu da ya samesu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amfanin Kuka

Mutane suna la'akari da kuka a matsayin gazawa, amma bincike ya nuna yin kukan na nuna wata hanaya da muatane suke samu wasu fa'idoji kamar haka:

1. Sa nutsuwa

A shekarar 2014 wani bincike ya nuna yadda kuka ke sa nustsuwa akan mutane. Binciken ya nuna yadda wata jijiya ke kumbura tare da sanyaya zuciya wadda take sawa mutum yaji sauki (shi yasa in mutum yana kuka yake nishi)

2. Taimako daga wasu

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Buhari Ya Yi Magana Kan Gaskiyar Bacewar Naira Tiriliyan 89 a Bankuna

Kuka na sa mutum ya samu taimako daga wasu, domin kuka kansa sa a bukaci taimakawa mutum.

3. Samun Sauki wajen rage radadi

Bincike ya nuna bayan samun sauki da nutsuwa, kuka na ragewa mutane radadin abinda yake damunsu.

Wannan hawayen da mutum yake fitarwa kan taimaka wajen samar da wani sauki daga abinda yake ji.

Kukaa
Amfanin Da ke Tattare Da Yin Kuka Bincike Daga Masana Harkar Hoto: Getty
Asali: UGC

4. Jin Nishadi da walwala

Kuka Kan sa Mutum yaji dama-dama watakila ma har ya dara daga abinda ya kurnace masa a zuciya. kuma wata hanyace da zai kusan duk abinda ke damunsa ya tafi

5. Fitar Da Sinadarai

Lokacin da mutum yaji bakin ciki ko wata damuwa, to yana tada wasu sinadarai a cikin jinkasa wanda su kuma su na fitane ta dalilin yin hawaye. Binciken ya nuna yadda mutum ke samun sauki da ga cutarwa da sinadarn kan oiya yi masa ba.

Kara karanta wannan

Elon Musk ya Saka Gadaje a Ofisoshi Twitter, Ya Ja Kunne Kan Sharholiya Babu Aiki Tukuru

6. Taimakawa wajen bacci

A wani dai binciken ya nuna yadda yara ke samun bacci musamman ma bayan sunyi kukan, yawanci bacci suke.

Sannan Kukan kan taimakawa yara su dawo taitayinsu daga wani firgici, shidewa ko yunwa da suka samu.

7. Yakar kwayoyin cuta

Akwai wasu kwayoyin cuta da idan mutum yana kuka suna ficewa daga idonsa, musamnan ma lokacin da yake hawaye to hawayen kan wankesu.

8. Kara Karfin Gani

Yawan yin kuka muraran kan taimakawa ganin mutm sosai, musamman ma in yana kuka yana kifta ido.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: