Baku Da Wani Yankan Hanzari Da Zai Sa Za Ace Baku Shirya Ba - Buhari Ga INEC
- Buhari yayi kira da hukumar zaben Nigeria sake dagewa dan tabattar da sahihin zabe. Yace basu da wani hanzari
- Buhari yace babu dalilin da zai hana hukumar zaben gudanar da zabe a Nigeria a shekarar 2022
- kasa da kwana tamanin da ɗoriya ya rage a gudanar da babban zaben Nigeria na shekarar 2023
America: Shugaba Buhari na kara tabbatarwa da duniya kudirinsa na tabbatar da anyi sahihi kuma nagartaccen zaɓe a Nigeria. Kamar yadda Premium Times ta rawaito
Wannan na zuwa ne ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace Buhari yayi wannan kalamin ne a birnin Washington DC, na ƙasar Amurka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Hukumar zaɓe ta shirya, sabida na tabbatar da mun basu duk wani abu da suka bukata, kuma na fada musu bana bukatar duk wani hanzari da zai sa ace akwai matsala"
Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa tun shekarar 2015 tsarin zaɓe ke ƙara inganta a Nigeria
"Daga shekarar 2019 manyan zaɓuka da kuma zabukan maye gurbi da suke inganta a Nigeria. Misali zaɓen Edo, Ekiti, Anambra da jihar Osun.
"Wannan Muke so mu gani a babban zaben shekarar 2023"
Buhari yace zai tabbatar da ɗorewar dimukuraɗiyya, da samar da mulki mai nagarta, dan tabbatar da an samu tsarin dorewarta a yankin nahiyar Afrika ta yamma.
Buhari ya cigaba da cewa wannan bazai samu ba har sai an tabbatar da an inganta rayuwar mutane, ta hanyar yakar talauci, rashin aikin yi da kuma tsaro.
Buhari Yayi Kira Ga Amuraka kan Goyan Bayan Hukumar Zaben Ƙasar Kan Yin Sahihin Zabe.
Buhari ya yi kira da gwamnatin Amurka su ci gaba da bamu hadin kai da goyan baya wajen tabbatar da sahihin zabe ta hanyar tallafawa hukumar zaben mu, dan samar da sahihin zabe a Nigeria da sauran kasashen Afrika.
Shugaba Buhari dai dare a karagar mulki ne, a shekarar 2015 bayan da gwada neman zaman shugaban kasar Nigeria din har sau hudu. Farawa daga shekarar 2003, 2007 da shekarar 2011 sai kuma shekarar 2015 da ya samu darewa.
Manyan masu neman takarar dai shugaban kasar Nigeria sune Alhaji Atiku Abubakar na PDP, da Bola Ahmed Tinubu na APC sai kuma Rabi'u Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na LP.
Asali: Legit.ng