Shugaba Buhari Zai Shilla Kasar Amurka Gobe Lahadi, Zai Kwashe Mako 1

Shugaba Buhari Zai Shilla Kasar Amurka Gobe Lahadi, Zai Kwashe Mako 1

  • Kimanin mako guda daga dawowa daga kasar Guinea, Shugaban kasa zai sake tafiyar kasar waje
  • Shugaban kasar Amurka ne ya gayyacesa, a cewar masu magana da yawin shugaban kasan
  • Kusan kowace shekara sai shugaba Buhari ya ziyarci Amurka halartan taron majalisar dinkin duniya

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba zai tafi birnin Washington, kasar Amurka domin halartan taron hadakar nahiyar Afrika da Amurka.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Asabar, rahoton DailyTrust.

Ya bayyana cewa za'ayi taron ne tsakanin ranar Talata, 13 ga Disamba zuwa 15 ga Disamba, 2022.

Buhari
Shugaba Buhari Zai Shilla Kasar Amurka Gobe Lahadi, Zai Kwashe Mako 1 Hoto: Preseidency
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, shugaban kasa Amurka, Joe Biden, ne ya gayyaci shugabannin kasashen Afrika.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Aike Sakon Gaisuwarsa Ga Sheikh Dahiru Bauchi

Ya ce wannan taron za'a yisa ne domin karfafa alakar nahiyar Afrika da Amurka wajen zuba hannun jari da sauransu.

Shugaba Buhari zai samu rakiyar wasu gwamnoni, ministoci, shugabanin hukumomin tsaro, da wasu manyan jami'an tsaro.

Gwamnonin sun hada da Gwamna Bala AbdulKadir Mohammed na jihar Bauchi da kuma AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara.

A karshe, ya ce shugaban zai dawo ranar Lahadi, 18 ga Disamba, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida