Hukumar Shirya Jarabawa Gama SIkandire Ta NECO Zata Fara Kai Jami'an Tsaro CIbiyoyin Jarabawa A Kasar

Hukumar Shirya Jarabawa Gama SIkandire Ta NECO Zata Fara Kai Jami'an Tsaro CIbiyoyin Jarabawa A Kasar

  • Satar amsa a jarabawar fita daga sikandire ta zama ruwan dare a tsakanin makarantu da dalibai
  • A wannann shekarar hukumar NECO ta sanar da rike sakamakon jarabawar wasu makarantu sakamakon zarginsu da satar jarabawa
  • Jami'an tsaron da za'a sa a makarantun zasu taimaka wajen magance yawan satar amsar da ake samu a makarantun

Abuja: Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta ce za ta kawo karshen satar jarrabawarta ta hanyar tura jami’an hukumar tsaron farin kaya da kare dukiyar al'umma (NSCDC) zuwa cibiyoyinta.

Haka nan ma hukumar ta ce za ta hada da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) domin shiga cikin lamarin.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ibrahim Wushishi wanda yake a matsayin babban shugaban hukumar NECO, ya bayyana irin ci gaban da aka samu a wajen wani taron karawa juna sani da aka gudanar a garin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Ana Sallar Isha’i, ‘Yan Bindiga Sun Harbe Liman, Sun Tasa Keyar Masu Sallah Babu Adadi a Katsina

Shugaban hukumar ta NECO ya yi kira da a hada karfi da karfe domin magance matsalar tabarbarewar jarabawa.

Wushishi ya ce akwai bukatar a gaggauta dakile matsalar domin tabbatar da ci gaban kasa baki daya.

“Daya daga cikin manyan kalubalen da ke kawo cikas ga gudanar da jarabawar shine yadda satar amsa ta zama ruwa dare a tsakanin makarantu da dalibai,” in ji shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Saboda haka, wannan taron bitar ya yi la’akari da hanyoyi da za a iya amfani da su don dakile wannan barna da ta zama kamar cutar daji".

NECOO
Hukumar Shirya Jarabawa Gama SIkandire Ta NECO Zata Fara Kai Jami'an Tsaro CIbiyoyin Jarabawa A Kasar
Asali: UGC

Wushishi ya cigaba da cewa:

“Wannan halaryar na hana hazikan ɗalibai yin aiki tukuru, da ragewa takardar shaidar darajar ta, da kuma samar yan kasa nagari, kuma hakan na shafar bukatun al’umma".
"Don haka dole ne mu dauki shawarar hada kai da jami'an tsaro don kawar da wannan mummunar dabi'a".

Kara karanta wannan

Bayan Shan Lugude da Gurfana a Kotu, Dalibin da ya Zolaya Aisha Buhari ya Koma Makaranta

Daga karshe dai Wushishi yace:

"Daga cikin jami’an tsaron Najeriya da muka amince muyi aiki da su sun hada da jami’an tsaro na Civil Defence wajen samar da tsaro a cibiyoyin jarabawa don hana miyagu/masu aikata munanan jarabawa,” in ji shugaban NECO".

Jarabawar NECO dai ana ajiyeta ne a wasu daga cikin bankunan kasar nan damin samar mata da tsaro da kuma rabata atsakanin makarantun da za'a gudanar a ranar domin tabbatar da an killace bayananta ba tare da sun fita ba

Hukumar Shirya Jarabawan NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2022

Shugaban Hukumar 'Dantani Wushishi shine ya sanar da csakin sakamakon jarabawar ababban ofishin hukumar dake a Minnar jihar Neja.

Wushishi yace sun dakatar da wasu makarantu guda biyar har tsawon shekara hudu, sakamakon samun satar jarabawa dumu-dumu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: