Kar Kuji Tsoron Fari Ko Rashin Abinci Shekara Mai Zuwa Inji Hukumar Kula Da Filayen Noma

Kar Kuji Tsoron Fari Ko Rashin Abinci Shekara Mai Zuwa Inji Hukumar Kula Da Filayen Noma

  • An samu ambaliyar ruwa sosai a jahohin arewa maso yamma a Nigeria wanda ake tunanin zai shafi abincin da za'a samar
  • Hukumar Kula da filin noma ta kasa tace akwai tanadin da tai wanda zai magance wannan matsalar karancin abinci da ake tunani
  • Kayan abincin dana masarufi sunyi tashin gwaron zabi a kasuwanni, sabidda karancin su da aka samu wannan shekarar

Abuja: Hukumar kula da filayen noma ta kasa NALDA ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa kasar ba za ta fuskanci matsalar karancin abinci ba a shekara mai zuwa, duk kuwa da irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a filayen noma fadin a kasar.

Hukumar ta ce, ta samar da fili eka 500 na noman alkama wanda za'ayi noman rani a jihohin Adamawa, Yobe, Jigawa, Gombe da kuma Taraba domin samar da abinci.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Atiku, Obi, Kwankwaso Suka Fada a Taron 'Yan Takaran 2023

noma da kiwo
Kar Kuji Tsoron Fari Ko Rashin Abinci Shekara Mai Zuwa Inji Hukumar Kula Da Filayen Noma Hoto: The Nation
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren zartarwa na hukumar, Prince Paul Ikonne ne ya bayyana hakan inda yace an kawar da matsalar karancin abinci a shekara mai zuwa, a wani rahotan jaridar The Nation

Ya kara da cewa hukumar a bana ta samar da injuna da kayan aikin noma a shiyyoyi shida na na kasar dan habaka samar da abincin.

Ikonne ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja inda ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin baje kolin nasarorin da NALDA ta samu cikin shekaru biyu da suka gabata.

A cewarsa, an samu gagarumin ci gaba wajen samawa matasa da mata aiyukan yi ta hanyar noma.

Ya kara da cewa:

"Shugaban kasar zai aza wani harsashi wanda hukumar zata yi aiki da manoma sama da 50,000 ban da kuma wanda zasu ci tallafin gajiyar filin kiwo".

Kara karanta wannan

Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa

Ya ce,

“NALDA ta dawo da aiyukanta sosai ne a kasan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da nufin karfafa gwiwar matasan Najeriya da su rungumi harkar noma, da magance matsalar filaye."
“A yanzu haka, muna samar da hekta 500 na noman alkama a dan noman rani kuma tun daga wannan lokacin har zuwa yau, NALDA na ci gaba da yin duk mai yiwuwa dan ganin an inganta rayuwar ‘yan Najeriya."
"Shugaban kasa zai bayyana abin da NALDA ke yi a cikin shekaru biyu da NALDA ta dawo don inganta rayuwar ‘yan Najeriya tare da bunkasa fannin noma.
“Shugaban kasa zai baje kolin wasu kayan aikin da NALDA ta siyo da kuma nasarorin da ta samu, da irin alfanun da ta samarwa yan kasa, duk da cewa baza mu iya zuwa gonakin dan mu nuna su ba amma dai akwai yanayi mai kyau da zamu tabbatar da hakan”. inji shugaban hukumar

Kara karanta wannan

Lauya Ya Fadi Dalili 1 da ya sa ‘Yan Sanda Janye Karar Mai 'Cin Mutuncin' Aisha Buhari

Hukumar NALDA Kafin Zuwan Buhari

A lokacin da muka karbi wannan gwamnati ta maigirma shugaban kasa ba ta gaji komai ba, walau kayan aiki ko kayan more rayuwa daga tsohuwar NALDA.
Amma kamar yadda muke magana a yau hukumar tana da ofisoshi a kusan dukkanin jihohin kasar nan 36 ciki har da babban birnin tarayya Abuja. .
"NALDA ta samu tiraktoci, kayan aikin gona, muna da gonaki a fadin shiyyoyin kasar nan guda shida, mun baiwa matasa 'yan Najeriya sama da 50,000 falayen noma da kayan aiki".

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida