Wani Matashi Mai Tarin Hikima Ya Kera Dankararen Gidan Laka da N1.3m, Bidiyon gidan Ya Yadu
- Wani matashi ya bayyana yadda yayi amfani da kudi kadan wajen gina hadadden gida na jan laka
- Wani bidiyo da Lawrance ya wallafa a TikTok a ranar 18 ga watan Oktoba ya nuna yadda aka fara ginin da kuma yadda aka kammala shi
- Masu amfani da TikTok da dama sun nuna sha'awarsu na son mallakar irin wannan gida yayin da bidiyon ya samu masu kallo fiye da 720k
Wani dan gajeren bidiyo da ke nuna sabon gida da aka gina da laka ya samu fiye da mutum 720k da suka kalle shi a dandalin TikTok kadai.
Wani matashi mai suna Lawrance wanda kwararre ne a fannin gine-gine shine ya wallafa bidiyon a dandalin a ranar 18 ga watan Oktoba.
Bidiyon ya dauki tsawon kimanin sakan 39 amma ya nuna yadda aka gina gidan tun daga tushe har zuwa rufin sama.
Bidiyo ya nuna hadadden gida da aka kera da laka da katakai
Abun da ya fi burgewa shine cewa Lawrance bai yi amfani da bulo din laka wajen kera gidan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maimakon bulo din laka, ya yi amfani ne da jan laka da katakai wanda daga baya ya yi shafe da siminti.
Masu amfani da TikTok da suka nuna sha'awar mallakar irin gidan sun tambayi nawa aka kashe a kai kuma Lawrance ya ce naira miliyan 1.3 (Ksh386,000).
Lawrance ya ce bai amfani da bulo din jan laka wajen gina gidan ba domin ya fi sauki da laka.
Bidiyon hadadden gidan ya kayatar da mabiyansa kan TikTok domin mutum fiye da 720k sun kalla, ya samu 'likes' fiye da 11k da martani 251.
Kalli bidiyon a kasa:
Masu amfani da TikTok sun yi martani
@Annet Sigowo ta ce:
"Gaba daya nawa ya kama? Karamin kanina na son yayi gini."
@vio_vk2 ta yi martani:
"Amma me yasa baka amfani da bulo din jan laka."
@El-shaddai ya ce:
"Ina bukatar daya a Ghana."
@bmw ya ce:
"Ina ganin ina bukatar wannan."
@patrickakoyo ta yi martani:
"Aiki ya yi kyau. Na so wannan."
Zaman Turai sai da juriya: Yar Najeriya ta ba da labarin yadda ta yi aikin goge-goge a UK duk da kasancewarta likita
A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya ta karfafawa masu yi balaguro zuwa Turai da su zamo masu juriya da hakuri a karonsu na farko.
Ta ce a lokacin da ta isa UK aiki na farko da ta fara yi a kasar shine na goge-goge duk da kasancewarta likita amma bayan shekaru da dama Allah ya musanya mata da alkhairi.
Asali: Legit.ng