Allah Yayiwa Uwar Gidan Wamakko Rasuwa Shugaba Buhari Ya Jajanta Masa

Allah Yayiwa Uwar Gidan Wamakko Rasuwa Shugaba Buhari Ya Jajanta Masa

  • Tsohon Gwamnnan jihar Sokoto, Alu Magatakarda wamakko Yayi Babban Rashi a Makon nan
  • Gwamnoni, Yan Uwa, Abokan Hulda, Yan Siyasa da mabiya na tururuwar yi masa ta'aziyya
  • Wamakko Ya rasa Uwargidansa ne shekaru biyu kacal bayan rashin diyarsa Sadiya

Abuja: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bisa rasuwar uwargidansa Hajiya Atika.

Shugaban kasar, a cikin sakon ta’aziyyar da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya rabawa manema labarai, ya ce ya labarin ya sosar masa rai.

Wamakko
Shugaba Buhari Ya Jajantawa Aliyu Magatardar Wamakko Bisa Rasuwar Matarsa hoto:Daily Trust
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin sanarwa da jaridar Daily Trust ta Samu, Garba Shehu yace:

"Rashin macen da ta kasance wani muhimmin bangare na rayuwar ku, kasancewarta uwar 'ya'yanku, yana da matukar zafi da za ku iya jurewa."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Matar Aure, Maryam, Ta Sheke Kishiyarta Kan Abu Daya a Arewa

“A yayin da kake alhinin rasuwar matarka mai kaunarka, ina mika sakon ta’aziyyata kan wannan rashin da ba za a iya misalta shi ba. Allah ya gafarta mata kurakuranta, kuma ya saka ta a aljanna. Allah ya jikanta ya bawa iyalanku baki daya hakurin rashinta, amin"

Lamarin ya zo ne shekaru biyu bayan Wamakko, tsohon gwamnan jihar Sokoto, ya rasa ‘yarsa Sadiya a watan Satumban 2020.

Daga cikin 'ya'yan data bari bari akwai Hindatu, Alhaji Muhammadu, Hauwa'u da barade

Wamakko Ya ja Hankalin Magoya Baya

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko, ya bukaci magoya bayansa a jihar Sokoto da kada su yi siyasar tada zaune tsaye, gabanin zaben 2023 mai zuwa.

Wamakko wanda kuma shi ne jigon jam’iyyar All Progressive Congress a jihar ya bayyana haka a gidansa na Gawon Nama da ke Sakkwato jim kadan bayan ya dawo daga Abuja.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Bashar Abubakar ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel