Korarren Akanta-Janar, Ahmed Idris, Ya Mayar Da Kudi N400m Cikin N84.7bn Da Ake Zargin Ya Sata

Korarren Akanta-Janar, Ahmed Idris, Ya Mayar Da Kudi N400m Cikin N84.7bn Da Ake Zargin Ya Sata

  • Ana cigaba da zaman shari'ar Akanta Janar na tarayya da aka fitittiki kan zargin almundahana
  • A kotu, wani mai bada shaida ya laburtawa Alkali yadda Ahmed Idris ya dawo da kusan rabin biliyan cikin kudin da ya wawura
  • Gwamnatin tarayya na tuhumar Ahmed Idris ya karkatar da kudin jihohi masu arzikin man fetur

Abuja - Babban kotun tarayya dake unguwar Maitama, birnin tarayya Abuja ta sake zama kan shari'ar zargin da ake yiwa korarren Akanta-Janar na tarayya, Ahmed Idris na satar kudin gwamnati.

A zaman ranar Talata, kotun ta ji yadda Ahmed Idris ya mayar da $900,000 (milyan dari hudu N400m) cikin kudi N84.7billion da ake zarginsa da wawura na kudin jihohi masu arzikin man fetur, rahoton TheNation.

Wani jami'in hukumar yaki da rashawa da yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC, Hayatudeen Ahmed, ya bayyana hakan yayin bada shaida a kotu.

Kara karanta wannan

N165bn sun dawo: CBN ya ce sabon kudi ya fara yawo, sabon batu mai muhimmanci ya fito

Ahmed idris
Korarren Akanta-Janar, Ahmed Idris, Ya Mayar Da Kudi N400m Cikin N84.7bn Da Ake Zargin Ya Sata
Asali: Facebook

Ana tuhumar Ahmed Idris, Godfrey Olusegun Akindele (wani dirakta a ofishin Akanta Janar) ; Mohammed Kudu Usman da kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited bisa laifin almundahanar N109bn.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shaidan ya bayyana cewa Alkalin cewa:

"Shi (Idris) ya dawo da $89,900 da kansa, wanda yanzu yana cikin, kuma yana cikin abubuwan da zamu gabatar matsayin hujja."

Ya ce cikin kudi N84.7b da ake zargin Ahmed Idris da rabawa tare da abokansa, an kwato N32bn kawo yanzu.

Ya kara laburtawa kotu yadda Idris ya dauki hayan tsohon hadiminsa, Akindele, wajen rabar da kudi N84.3bilion cikin N84.7b.

Yace daga baya Akindele ya baiwa Idris la'adan N4.2bn albarkacin bashi aikin rabon kudin.

Lauyoyin Idris sun ki yarda

Lauyoyin Ahmed Idris – Chris Uche, Joe Abraham, Mohammed Ndayako da Gordy Uche sun ki yarda Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs, ya gabatar da kudin da ya dawo da su matsayin hujja gaban alkali Yusuf Halilu.

Kara karanta wannan

Kowa Ya Kai Tsaffin Kudinsa Banki, Ba Zamu Kara Wa'adin Ko Minti Daya Ba: CBN

Amma Alkalin yayi watsi da su kuma ya amince da jawabin matsayin hujja.

Duk da haka, Lauyoyin Idris sun ki yarda Alkalin ya amince da jawaban da Ahmed Idris yayi lokacin yana hannun EFCC, sun ce tilasta fadinsa akayi.

Sakamakon haka suka bukaci Alkalin ya shirya zama na musamman don tabbatar da gaskiya lamari shin tilastasa akayi ko da son kansa ya fada.

An dage zaman zuwa ranar 30 ga Junairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida