Makiyayi Ya Kashe Dan'uwansa Bafulatani, Ya Jefa Gawarsa Cikin Buhu Kuma Ya Sace Dabbobinsa

Makiyayi Ya Kashe Dan'uwansa Bafulatani, Ya Jefa Gawarsa Cikin Buhu Kuma Ya Sace Dabbobinsa

  • Wani labari mai sosa zuciya daga jihar Enugu inda ake zargin wani Fulani da kashe dan'uwansa Fulani
  • Bidiyon da aka watsa a kafafen sadarwa yace al'ummar unguwa a Ezaeagu ne suka kamashi
  • Hoto ya nuna mutumin tsare cikin motar yan sandan yankin Ezeagu dake jihar Enugu, kudu maso gabas

Enugu - Wani bafulatani da ake kyautata zaton makiyayi ne ya shiga komar yan sandan Najeriya kan zargin kashe dan'uwansa Bafulatani tare da sace dabbobinsa a jihar Enugu.

SaharaReporters ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne a garin Imama, karamar hukumar Ezeagu ta jihar ranar Laraba.

Ana zarginsa da kashe mutumin tare da jefa gawarsa cikin jaka kuma ya daura kan babu dinsa yana kokarin kaita inda zai jefar yayinda mutan unguwa suka damkeshi.

Daga baya aka mikashi ofishin hukumar yan sanda dake Ezeagu.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari Ya Kaddamar, 'Yan Najeriya Sun Maida Martani Game da Sabon Sumfurin Kudin Naira

Ezeagu
Makiyayi Ya Kashe Dan'uwansa Bafulatani, Ya Jefa Gawarsa Cikin Buhu Kuma Ya Sace Dabbobinsa Hoto: @saharareporters
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mazaunin unguwar a jawabin da yayi yayin daura faifan bidiyon labarin a wani shafin yan asalin jihar Enugu ranar Laraba yace:

"Dubi yadda Fulanin nan ke tada rikici a unguwannin Enugu don Sojoji su kawo mana hari."
"Wannan Fulanin dake cikin motar yan sandan ya kashe dan'uwansa Fulani kuma ya kwashe shanunsa."
"An gansa kuma aka kama shi sannan aka mikashi hannun yan sanda. Wannan abu ya faru a Ezeagu."

An yi yunkurin jin ta bakin Kakakin yan sanda jihar Daniel Ndukwe amma abin ya ci tura.

'Ramuwar Gayya Muka Yi': Kotu Ta Yanke Wa Wasu Makiyaya Uku Hukunci Kan Ƙone Gonar Gyaɗa Ta Miliyan N1.5m

A wani labarin kuwa, Kotun Majistire dake zama a jihar Kebbi ranar Talata ta umarci a tasa ƙeyar wasu Makiyaya uku zuwa gidan gyaran hali bisa zargin ƙone Gonar Gyaɗa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Gonar da ake zargin makiyayan sun ƙone ta kai darajar kuɗi N1.5m.

Waɗanda ake zargin da suka haɗa da, Riskuwa Mode, Manu Kinasa da kuma Sanda Kiruwa, an ce sun cinna wa Gonar wuta da gangan a ƙauyen Mashekari Geza, ƙaramar hukumar Bunza a jihar Kebbi.

Alkalin Kotun mai shari'a Hassan Muhammad Kwaido, ya nemi jin maƙasudin ƙone Gonar daga bakin waɗanda ake zargi kuma a bayanansu sun ce abinda suka yi ramuwar gayya ce kan abinda mai gonar ya aikata musu bara.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: