Shugaba Muhammadu Buhari Zai Sake Tafiyar Kasar Waje Gobe
- Mako daya daga dawowa daga Landan, shugaba Muhammadu Buhari zai sake fita daga Najeriya
- Akalla manyan jami'an gwamnati shida ne zasu takawa shugaban kasan baya zuwa Nijar
- Gwamnatin kasar Nijar ta kammala ginin wani titin da aka sanyawa sunan Shugaba Muhammadu Buhari
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a gobe Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, 2022 zai yi tafiyar zuwa birnin Niamey, babbar birnin kasar Nijar domin halartan taron gamayyar kasashen Afrika.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana hakan ranar Laraba.
Yace shugaban kasa kuma zai halarci taron kaddamar da wani littafi da aka rubuta kansa wanda aka fassara zuwa harshen Faransa da kuma kaddamar da titin da Gwamnatin Nijar ta sanyawa sunansa.
A cewarsa, Farfea John Paden na jami'ar George Mason dake Amurka ne ya rubuta littafin.
Ya ce Buhari zai kaddamar da titin kafin taron gamayyar kasashen Afrikan ranar Juma'a, 25 ga Nuwamba, 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Garba Shehu yace Buhari zai smau rakiyar;
- Minista harkokin waje, Geofrey Onyeama
- Ministan TSaro, Bashir Salihi Magashi
- Ministan Masana'antu, Adeniyi Adebayo
- Ministar Kudi, Zainab Shamsuna
- NSA Babagana Monguno
- DG NIA, Ambasada Ahmed Rufa'i
Yace Buhari dawo ranar Juma'a ba kakkautawa.
Asali: Legit.ng