Yan Awanni Daga Sakoshi Daga Kurkuku, An Sake Kamashi Yana Sata
- Jami’an yan sanda sun sake damke wani barawo yan awanni daga fitowarsa daga gidan yari a jihar Legas
- Kakakin hukumar yan sandan jihar yace wasu bayin Allah ne suka biya masa kudin tarar da kotu tayi masa amma kuma ya koma ruwa
- Yan Najeriya a kafafen ra’ayi da sada zumumta sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan abu da matashin yayi
Lagos - Hukumar Yan Sanda ta sake damke wani matashi kan zargin sata ‘yan sa’o’i bayan fitowarsa daga kurkuku inda aka jefashi kan laifin aikin bera.
Jami’an rundunar Rapid Response Squad (RRS) dake jihar Legas a ranar Asabar sun damke matashin ne bayan ya fasa cikin wata ma’aikatar gwamnatindon satan kayan karafuna.
Kakakin hukumar yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Alhamis.
Soji sun Halaka Kachalla Gudau, Kwamandan ‘Yan Bindiga da Ya Shahara a Satar Shanu da Dillancin Kwayoyi
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
“Jami’an RRS da safiyar Asabar suka kama wani tsohon barawo yan awanni bayan sakoshi daga kurkuku.”
“Matashin mai suna Yakub Yusuf dan shekara 23 ya shiga hannu ne misalin karfe 8 na safiya bayan yanke masa hukuncin wata guda a Kurkuku kan laifin sata gidan fetur na Legas dake Alausa, Ikeja.”
“Ganin an garkameshi ne saboda ya gaza biyan tara, wata kungiyar jin kai ta biya tarar da aka masa ranar Juma’a 11 ga Nuwamba, kwana goma bayan garkamesa a Kurkuku ranar 1 ga watan Nuwamba.”
Kakakin yan sanda ya kara da cewa sakinsa ke da wuya ya sake kai hari cikin ofishin hukumar kwana-kwana ta jihar Legas inda ya sace marufin karfe tsaffin motocin kashe wuta da ake gyarawa.
Kwamandan rundunar RRS, CSP Olayinka Egbeyemi ya mika shi ga sashe SCID don gudanar da bincike mai zurfinkansa.
An Gurfanar Da Abubakar A Kotu Kan Satar Burodi A Kaduna
A wani labarin kuwa, an gurfanar da wani matashi dan shekara 25, Abubakar Muhammad, ranar Alhamis a kotun Shari'a dake Magajin Gari, jihar Kaduna kan laifin satar Burodi.
Baya ga Satar Burodin, an tuhumcesa da laifin dabawa mai sayar da da Burodin, Isah Hamza, wuka.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Abubakar da farko ya musanta tuhumar da ake masa kuma aka bashi beli.
Asali: Legit.ng