Magidanci Ya Garkame Matarsa na Shekara 1 a Yobe, Yana Fuskantar Bincike

Magidanci Ya Garkame Matarsa na Shekara 1 a Yobe, Yana Fuskantar Bincike

  • Rundunar ‘yan sanda ta jihar Yobe ta sanar da fara bincike kan wani magidanci da ake zarginsa da garkame matarsa na tsawon shekara 1 tare da hana ta abinci sai koko
  • Kamar yadda aka gano, mahaifiyar matar ta dade bata ji daga diyarta ba, hakan yasa ta tashi daga Kano zuwa Nguru inda ta tarar diyarta na gargarar mutuwa
  • Tuni ta fallasa lamarin inda ta dauka Sadiya zuwa asibiti tare da kira ga ‘yan sanda da su kama magidancin da gurfanar dashi

Yobe - Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta fara bincike kan zargin da ake yi wa wani magidanci mai suna Ibrahim Bature da garkame matarsa mai suna Sadiya tare da hana ta abinci a gidansu dake yankin Nguru a jihar na tsawon shekara daya.

Taswirar jihar Yobe
Magidanci Ya Garkame Matarsa na Shekara 1 a Yobe, Yana Fuskantar Bincike. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Kara karanta wannan

Ba Zan Iya Kusantar Namiji Ba: Kyakkyawar Budurwa Da Aka Nadawa Sarauta Ta Magantu, Bidiyon Ya Janyo Cece-kuce

Jaridar Punch ta rahoto cewa, majiya daga yankin tace mahaifiyar yara hudun tana rayuwa ne da shan kamu.

An gano cewa mahaifiyar Sadiya mai suna Hadiza ce ta cece ta bayan kwashe tsawon lokaci da tayi bata gan ta ba, don haka ta tashi takanas daga Kano har gidanta dake Nguru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan ganin diyarta cikin mawuyacin hali, Hadiza ta lura cewa bata iya ko tafiya kuma yunwa tana dab da yin ajalinta.

Fusatacciyar mahaifiyar ta fallasa lamarin tare da hanzarta mika Sadiya zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano domin samun taimakon gaggawa.

Jaridar Newswire ta rahoto cewa, Hadiza tayi kira da a kama Bature tare da gurfanar dashi inda ta kara da cewa gwamnatin jihar ta saka baki kan lamarin.

’Yan sanda sun magantu

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abdulkarim Dungus, yace rundunar ta fara bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kyakkyawa Ce: Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Ji Da Tsawo Sanye da Takalma Masu Tsini a Ran Aurenta Ya Ja Hankali

Yace:

“DPO din Nguru ya gayyaci mijin jiya domin ya taimaka kan bincike. Matar a halin yanzu tana samun kulawa a asibiti dake Kano. Za mu yi bincike ingantacce, mu ji daga kowanne bangaren kafin mu zanta da ‘yan jarida.”

Ba wannan bane karo na farko da aka fara jin makamancin haka

A wasu labarai, an ji yadda ake garkame mutane na shekaru masu yawa ba tare da wata kulawa ba ko abincin da ya dace.

A jihar Kebbi an samo karamin yaron da matar mahaifinsa ta garkame tsawon shekaru bata bashi abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: