Ibeto, Attajirin da Ya Shigo da Kwantena 65 a Rana 1, Zai Iya Zarce Dangote a Kudi
- Cletus Ibeto ‘dan kasuwa ne daga karamar hukumar Nnewi na jihar Anambra wanda ya so zuwa makaranta amma ya kare a kasuwancin bangararorin ababen hawa
- Ya kafa kamfani mai suna Ibeto Group wanda ke samar da siminti, bangarorin ababen hawa da sauransu duk domin siyarwa
- Ya mallaki kamfanin makamashi kuma ya shiga yarjejeniya ta maja da wani kamfanin Amurka domin kamfanin simintinsa ya shiga kasuwar duniya
Sunayen marasa yawa ne ke tasowa sama a Najeriya idan aka yi batun samar da siminti a Najeriya. Simintin BUA, Dangote da kuma Ibeto.
Sunan kamfanin simintin Ibeto suna ne da ake ji tun kafin zuwan kamfanin BUA da Dangote a bangaren siminti.
Tushen mai kamfanin
Mallakin Cletus Ibeto, kamfanin siminti na Ibeto yayi suna ballantana a kudu maso gabas tun kafin shigar Dangote kasuwar simintin, ya murkushe farashin tare da mamaye masana’antar baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An haife shi a ranar 6 ga watan Nuwamban 1952 kuma ‘dan asalin Nnewi ne dake jihar Anambra. Ibeto ya so yin ilimi har zuwa matakin digiri kuma ya so zama wani abu.
A maimakon hakan kamar yadda Nairametrics ta rahoto, mahaifinsa yana da wani shiri na daban a kansa domin ya koyi sana’a.
A yayin da yake shekaru 13, matashi Ibeto ya je ya fara koyon aiki a karkashin Akamelu, wani ‘dan kasuwar bangarorin ababen hawa a Onitsha.
Ya samu kansa karkashin horarwar Akamelu a inda ake kiransa da yaron Ibo.
Yadda ya koyi sana’a
Bayan nakaltar yadda ubangidansa yake tsarin aikinsa da komai, ya bar koyon aikin yayin da aka fara yakin basasa.
Ya koma bayan shekaru da dama inda ya bude shagonsa tare da fara kafa kamfani mai suna Ibeto Trading Company wanda ake shigo da batiran motoci da sauran sassan motoci.
Ya kafa kamfani a Nnewi kuma zuwa 1988, ya mamaye bangaren shigo da kayayyaki da suka shafi bangarorin ababen hawa.
A cikin shekaru 10, kamfaninsa ya gawurta inda ya zama mafi shahara a Afrika wurin samar da bangarorin ababen hawa.
Shahararsa ta kara kamari tun bayan da gwamnatin Shehu Shagari ta samar da dokar hana shigo da kayayyaki babu lasisi.
A yayin da wasu suka dauka hutu daga shigowa da kayayyaki saboda sabon tsarin, Ibeto ya shiga kai tsaye kuma ya kashe N3 miliyan domin samun lasisi wanda ya bashi damar shigowa da kwantena 65 a lokaci daya.
Sauran masu irin kasuwancin sun ji jiki yayin da suka yanke hukuncin neman lasisin shigo da kaya daga baya.
Adana kudi a akwatuna don bankuna
Ibeto ya bayyana cewa yana amfani da akwatuna wurin adana kudi don bankuna. Duk da tsadar kayansa sun Karu da wurin kashi 500, jama’a sun cigaba da siyensu inda aka ce ya samu kudin da suka kai fam miliyan hudu kwanaki hudu bayan zuwan kwantenoninsa.
Wannan ne ya bashi damar fara kafa kamfaninsa a Nnewi.
A 1996, Ibeto ya kafa kamfaninsa a Nnewi mai suna Ibeto Petrochemical Industries Limites wanda yake samar da jerin kemical da mayuka na amfanin gida da kasashen ketare.
Ibeto ya koma makaranta
Bayan dukkan gwagwarmaya da yayi fama da ita, ya koma makaranta inda ya samu kwalin kammala sakandare yana da shekaru 48 kuma ya karanci fannin kudi a jami’ar Najeriya dake Nsukka yayin da yake da shekaru 54 a duniya.
An bashi digirin digirgir na karramawa daga UNN.
Asali: Legit.ng