Nayi Matukar Takaicin Tarwatsewar Nigeria Airways, Matukin Jirgin Sama na Farko a Najeriya

Nayi Matukar Takaicin Tarwatsewar Nigeria Airways, Matukin Jirgin Sama na Farko a Najeriya

  • Kyaftin Bob Hayes, matukin jirgin sama na farko a Najeriya, ya bayyana irin takaicin da ya shiga bayan rushewar Nigeria Airways
  • Haifaffen jihar Benin din mai shekaru 87 a duniya, yace yunkurin gwamnatin nan na kafa sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya abun yabo ne
  • Sai dai tsohon ministan sufuri, Chif Anthony Okpere ya bayyana irin wahalar da wasu ma’aikatan suka shiga bayan rushewar Nigeria Airways da kin biyansu kudadensu

Matukin jirgin saman Najeriya ba farko, Kyaftin Bob Hayes yace rushewar tsohon kamfanin jiragen sama na Najeriya ne ya matukar bakanta masa rai da sauran ma’aikatan kamfanin, Daily Trust ta rahoto.

Hayes Bob
Nayi Matukar Takaicin Tarwatsewar Nigeria Airways, Matukin Jirgin Sama na Farko a Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya yabawa gwamnatin Najeriya

Yace yunkurin sake kafa sabon kamfanin jiragen sama da gwamnatin tarayya ke yi abun yabo ne inda yace Najeriya ta cancanci hakan matsayinta a Afrika.

Kara karanta wannan

Hotunan Matashin da Ya Kera Masallacin Karamin Masallacin Ka’aba a Borno Ya Birge Jama’a

Haifaffen jihar Benin din mai shekaru 87 yayi magana da manema labarai ne a wata liyafa da tsohon Injiniya da kamfanin jiragen saman Najeriya, Chif Anselm Kayode Mohammed ya shirya domin karramasa a kwanakin karshen makon da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa, liyafar ta hada manyan mutane masu tarin yawa wadanda tsofaffin ma’aikatan kamfanin jiragen saman Najeriyan ne.

Yace masana’antar tana samun cigaba kuma akwai yuwuwar ta cigaba yayin da yake yabawa wadanda suka karrama shi.

Hayes yace:

“Ban taba tsammanin wannan ba amma ina godiya ga Ubangiji da yasa wannan damar tazo kuma ina fatan wannan ta zama tushen abubuwa masu kyau.
“Ina tunanin masana’antar tana samun cigaba mai tarin yawa kuma na yarda cewa nan gaba za a samu wani cigaban kuma ina alfaharin cewa ina cikinta tun farko har nake da damar duba cigaban. Muna fatan samun cigaba a bangaren.”

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Kamar yadda yace, shirin gwamnatin tarayya na samar da wani kamfanin jiragen saman mai suna Nigerian Air, abun yabo ne.

Yace:

“Mun matukar takaici lokacin da muka rasa Nigeria Airways. Amma yanzu da ake kokarin samar da sabo, ina tunanin yana daya daga cikin abubuwa masu kyau da zasu faru a kasar nan.
“Da yawan kasashen Afrika yanzu suna da kamfanonin jiragen samansu kuma ina tunanin lokacin Najeriya a matsayinta na gwarzuwar Afrika, da zaka ja ragamar sauran kasashen a wannan masana’antar. Najeriya ta cancanci hakan kuma ina fatan hakan ta faru.”

Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma tsohon manajan daraktan Nigeria Airways, Chif Anthony Okpere ya jaddada cewa bai dace kamfanin ya mutu ba.

“A lokacin da aka siyar da Nigerian Airways, dukkan ma’aikatan sun shiga wani hali, da yawansu ba a biya su ba, wasu sun mutu kafin gwamnatin Buhari tazo ta biya su.
“A gaskiya hakan bai dace ba. Yanzu a yayin kafa sabon kamfanin, ban san siyasar dake kunshe da hakan ba, ban san shawarar da suka samu ba.

Kara karanta wannan

Yadda Wata Budurwa Yar Shekara 18 Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta Yar Shekara 60

“Sun fara sabo amma sanin inda zai kai ne babu wanda yayi.”

- Yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel