Almundahanar N19m: Bayan Kwace Kadarorinsa 5, An Damke Odito-Janar A Jihar Yobe
- Hukumar EFCC ta gurfanar da Odito-Janar na kananan hukumomi a Damaturu kuma ta kwace dukiyarsa
- Babbar kotun tarayya ce ta bada umurnin sadaukar da wasu manyan kadarorinsu guda biyar
- Alhaji Yahaya Wakil-Idris ya gurfana ne bisa laifin karkatar da kudaden gwamnati da almundahana
Yobe - Mutumin da ke da hakkin tabbatar da gaskiya kan kudaden da kananan hukumomi suka kashe a jihar Yobe ya sake gurfana a kotu ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, 2022.
Hukumar hana almundahana EFCC ta gurfanar da Yahaya-Wakil Idris ne gaban Alkali Mohammed Lawan bisa laifin almundahanar kudi N19,900,000.00.
EFCC tace a 2017, Wakil ya karbi kudi milyan 19 kuma ya sayi Mota Toyota Corolla 2015 kuma ya zaftare milyan 10.
Ya Musanta Zargin EFCC
Mutumin ya bayyanawa kotu cewa shi dai bai aikata laifin da EFCC ke zarginsa da shi ba, rahoton TheNation.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lauyan EFCC, J. A Ojogbane ya bukaci kotu ta dage zaman zuwa wata rana.
Amma Lauyan Wakil, Baba Zau ya bukaci kotu ta bada belin wanda yake wakilta kafin a dawo.
Daga karshe Alkalin ya bada belinsa kan kudi N2m da wata kadara dake Damaturu.
An dage zaman zuwa ranar 30 ga Nuwamba 2022.
Hukumar tuni ta garkame wasu kadarorinsa guda biyar bisa zargin babakere da ta'annuti.
Dukiyoyin sun hada da rukunin gidaje mai 20 dake bayan Sector II Operation Hadin Kai Headquarters a Damaturu, FARSAWA Plaza dake gaban bankin First Bank dake titin Gashua, wani kanti da ake kan ginawa gaban bankin CBN Damatruru titin Gujba; rukunin gidaje da kuma wani gida dake Nyarnya.
A Sankamo mana AA Zaura, Kotu ta umurci EFCC
Kotun tarayya dake zamanta a jihar Kano ta umurci hukumar EFCC ta gurfanar da dan takarar takarar sanatan APC a Kano ta tsakiya, AA Zaura gaban kotu.
Ana zargin AA Zaura ne da laifukan da suka shafi almundahana da damfara.
Mai shari'a Mohammed Nasiru Yunusa ne ya ba da wannan umarni a ranar Alhamis bayan da masu shigar da kara suka shaidawa kotu cewa, dan takarar na APC bai halarci zaman kotu ba a zaman da aka yi sau biyu.
Asali: Legit.ng