Yan Sanda Sun Saki Tinkiyar Da Aka Kama Da Laifin Cin Bushasshen Kifi a Borno

Yan Sanda Sun Saki Tinkiyar Da Aka Kama Da Laifin Cin Bushasshen Kifi a Borno

  • An sako tinkiyar da aka kama da laifin cinye kifin mai suyan kifi a Maidugurin jihar Borno
  • Dattawan unguwa sun baiwa mai sayar da kifin hakuri kuma daga karshe ya amince ya yafe
  • Wani dan siyasa ya yiwa mai sayar da kifin kyautar naira dubu hamsin albarkacin hakurin da yayi

Maiduguri - Hukumar yan sanda a jihar Borno ta saki Tinkiyar da aka damke kan laifin cinye bushasshen Kifin wani dan kasuwa, Malam Yusuf Ibrahim, a unguwar Bulabulin Maiduguri, jihar Borno.

Mai tinkiyar, Luba Mohammed, ya bukaci dattawan unguwa su tayashi baiwa Mai Kifi Ibrahim hakuri.

Ibrahim, mai sayar da kifin da kai karar Tinkiyar caji Ofis ya bayyanawa manema labarai cewa dattawan unguwa sun bashi hakuri kuma ya hakura, rahoton Zagazola.

Amma dai ya bada sharruda wanda ya hada da kada hakan ya sake faruwa.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Maikifi
Yan Sanda Sun Saki Tinkiyar Da Aka Kama Da Laifin Cin Bushasshen Kifi a Borno Hoto: @ZagazOla
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An saki Tinkiyar ranar Lahadi a hedkwatar yan sanda dake Bulabulin.

Bugu da kari, wani mamban kwamitin kamfen jam'iyyar APC, Hanarabul Husseini Monguno, ya baiwa mai kifin kyautar N50,000 saboda hakurin da yayi.

Laifin Me Tinkiya tayi

Tun farko dai Mai sayar da Kifi soye Malam Yusuf Ibrahim ya shigar da kara ofishin hukumar yan sanda bisa yadda tinkiyar Malam Luba Mohammed ke tafka masa barna ba kakkautawa.

Ibrahim ya bayyana cewa ya dade yana yiwa Luba gargadi bisa wannan asara da Tinkiyarsa ke janyo masa, rahoton DailyTrust.

A cewarsa, mai tinkiyar bai dawo wani mataki kan hakan ba kuma ya sa ya yanke shawarar kai kara wajen hukumar.

Kalli martanin mabiyansu a soshiyal Midiya:

Mariya M Aliyu tace:

"Nidai nace Duniyar Nan ba Gaskiya a Tuntu6i lubatu me timkiyar Nan, Anya ba lauje cikin Nadi,, ace Tinkiya harda Dan gwalar yaji"

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Asmau Adam tace:

"Tirkashi dabbar ma sukunyi magana Akai lallai wannan tinkiyar kin jawo magana"

Saifullahi Nura yace:

"Alanguburo fa abun nata kullum Kara gaba yake"

Yahaya Sabo yace:

"Ai dabbobin zamanin nan na yanzu shegu ne, Alaji kamar mutane haka su ke. Domin yanzu haka mu a nan unguwarmu gidan da idan basu sami almajiran da za su debo musu ruwa ba akuyoyin akwai gidan ake bawa butikai su je su debo, ko wani siyan kayan miya ko kuma wani aiken idan ba yaro a kusa duk su suke yi"

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida