Malami Dan Najeriya, Sheikh Adam Al-Fulany Ya Lashe Gasar Adabin Larabci a Maroko
- Sheikh Adam Abdurrrahman Al-Fulany, Malamin Adabin Larabci Dan Najeriya Ya lashe gasar Larabci a kasar Maroko
- Mutane sun yi mamakin yadda dan Najeriya ya kada Larabawa wajen gasar Uyoon El-Adab El-Arabi
- Za'a gudanar da taron karrama Malamin wanda mazaunin jihar Kano ne a kasar Magrib a Nuwamba
Malamin Dan Najeriya kuma mazauni jihar Kano, Adam Abdurrahman Al-Fulany, ya zama gwarzon ilmin adabin larabci na shekarar 2022 na Uyoon El-Adab El-Arabi dake Kasar Maroko.
An karrama Malamin bisa ayyukan rubuce-rubucen da yayi wanda ya shafi adabi, tarihi, al'ada dss.
Za'a baiwa Al-Fulany kyauta na nasarar da ya samu a taron Uyoon El-Adab El-Arabi da za'ayi ranar 1 ga Nuwamba, 2022 a birnin Uyoon, Maroko.
Wane ne Al-Fulany?
Malamin a 2021 ya lashe kasar adabin larabci na Hamsa dake Kahira, babbar birnin kasar Masar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cibiyar nazarin yaren Larabci ta Najeriya ce ta zabeshi don a bashi wannan kyauta.
An haifeshi ranar 30 ga Junairu, 1963, inda ya halarci makrantar Sakandaren Darul Ulum Ilori jihar Kwara da Markazul Duruusul Arabiyya dake Agege jihar Legas.
Ya samu digiri a ilmin adabin larabci daga jami'ar Bayero dake Kano a 1992 sannan ya yi Majistir a ABU Zaria a 1994.
Littafan da ya rubuta
Daga cikin littatafan da ya rubuta akwai:
Raai Al-Ganam
Ahl Al-Takror
‘Alat-Tariq
Jamiah Alarwah
Al-Gaibiyyat ala Dao’i Al-Ilm was Al-Deen
Muhimmah Al-Insan Ala Sath Al-Ard
Sira Al-Ajyal fi Qadaya Al-Islam
Hadithun maa Ulama Al-Hadith
Asali: Legit.ng