Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

  • Saura yan watanni wa'adin gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zo karshe
  • Uwargidarsa ta yi tsokaci kan dalilin da yasa ta baiwa yan Najeriya hakuri a sakon Oktoba 1 din ta
  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa shi dai ya cika alkawuran da ya yiwa yan Najeriya cikin shekaru 7

Hajiya Aisha Buhari, uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana dalilin da ya sa ta bukaci yan Najeriya su yiwa gwamnatin mijinta afuwa.

A hirar da tayi da BBC, Aisha tace dubi ga irin burace-buracen da 'yan Najeriya suka ci a kan gwamnatinsu, da alamun gaskiya ba'a biya musu buƙatunsu ba.

Zaku tuna rahotannin cewa Aisha Buhari ta nemi afuwar yan Najeriya bisa halin takaici da wahalhalun da suka shiga karkashin gwamnatin maigidanta.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Aisha
Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Yayinda aka tambayeta shin me yasa ta nemi wannan afuwa, tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Burace-buracen da aka dora kanmu na da yawa. Mutane sun sa ran samun abubuwa da dama a mulkinmu, kuma wataƙila bayan shekara bakwai bamu cika musu burikan ba."
"Allah kaɗai ya san abin da ke zuciyar mutum. A matsayinka na ɗan Adam, ba za ka iya cewa ka yi daidai ba, ko kuma ka ce ka yi abin da ya kamata. Saboda haka gwamnatin sun yi ƙoƙarin gaske, amma wasu zasu ga sun yi kasa a gwiwa."
"A nasu (gwamnati) suna ganin sun yi ƙoƙari, Allah ne mafi sani. Saboda haka dole mu da haƙuri ko da mun cika musu burinsu ko ba mu cika ba."

Na Cika Alkawuran Da Na Yiwa Yan Najeriya Cikin Shekaru 7, Buhari

A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron bita kan ayyukan da Ministocinsa sukayi cikin shekaru 7 da suka gabata tun da ya hau mulki.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lallai ko shakka babu ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa al'ummar Najeriya.

Taron ya samu halartan tsohon shugaban kasar Kenya, Uhurru Kenyatta, rahoton Leadership.

Shugaban kasan ya bayyana irin nasarorin da ya samu a bangaren aikin noma, gine-gine, tsaro, kiwon lafiya, yaki da rashawa, dss.

Saura yan watanni wa'adin gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zo karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida