Matashi Ya Hallaka Kansa Sakamakon Bayani Barayi Sun Sace Masa Keke Napep 2
- Wani direban Keke Napep ya aika kansa barzahu sakamakon takaici da bakin cikin abinda ya faru da shu
- A karo na biyu, barayi sun sace mota mai kafa uku da aka bashi 'Hire Purchase' don ya nemi abinci
- An yi jana'izarsa ranar 15 ga watan Oktoba, kwanaki biyu kacal bayan mutuwarsa
Wani matashi dan shekara 25, Bulus Asuma, a garin Jos, jihar Plateau ya dauki ran kansa sakamakon halin kunci da ya shiga na sace keken adaidaita sahu na Haya karo na biyu.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito hukumar yan sandan jihar da bayyana hakan ranar Laraba.
Matashin wanda mazaunin Anguwan Rukuba ne a Jos ya rataye kansa cikin daki bayan wasu barayi sun kwace Keke Napep na biyu kuma duka na 'Hire Purchase'.
Wani dan'uwan mamacin, Mr Adukuchili Angai, ya bayyanawa NAN cewa Asuma ya kashe kansa ne saboda takaici da kuncin rayuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An kwace masa Keke na farko
Angai yace kwanakin baya aka kwace Asuma Keke na farko kuma yanzu haka yana kan biyan bashin kudin ne.
A cewarsa:
"Da farkon shekarar nan, Asuma ya samu Keke Napep na haya wajen wata mata da sharadin ya rika balans mako-mako, sai ya baiwa abokinsa aro kuma aka sace."
"Matar ta sa aka damkeshi kuma sai da yayi mako guda hannun yan sanda kafin aka sakeshi kuma aka ce sai ya biya dukka kudin inda akayi yarjejeniya zai biya mako-mako."
"Bayan yan makonni ya fara gajiyawa, sai ya bukaci wani ya sake bashi Keke don ya samu ya biya bashin na baya. Amma yayi rashin sa'a inda a ranar 13 ga Oktoba yana kanyar komawa gida wani dan fashi ya kwace."
"Ya dawo gida cikin takaici kuma ya fadawa abokansa cewa kawai zai kashe kansa."
Angai ya cigaba da cewa abokan basu dauka da gaske yake ba, sai washegari aka leka dakinsa aka ga ya rataye kansa.
Asali: Legit.ng