Rikici Ya Barke Tsakanin Limami Da Kwamiti: Gwamnan Ondo Ya Rufe Babban Masallacin Jihar
Ikare - Gwamnatin jihar Ondo ta garkame babban Masallacin Ikare Central sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakanin Babban Limamin, Sheik Abubakar Muhammad, da majalisar Musulman Ikare.
Ikare na karamar hukumar Akoko North East ta jihar Ondo.
Majalisar tare da Sarkin garin, Okukare of Ikare, Saliu Momoh IV, sun sallami Limamin, amma kwamitin Limamai da Malaman addini a kasar sun sam ba zasu yarda da tsige limamin ba.
Yanzu haka ana tashin tashina a garin game da wannan lamari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Premium Times ta ruwaito cewa Shugaban kwamitin majalisar, Adewale Abayomi, da Sakatare R. AiyeGbusi sun baiwa Imam Abubakar Muhammad takardar sallama ne ranar 10 ga Oktoba, 2022.
A ranar Juma'ar da ta gabata, da taimakon jami'an tsaro aka Sallaci sallar Juma'a.
Amma duk da yunkurin sulhun da ake kokarin yi, kwamitin ta lashi takobin sai Limamin ta tafi.
Gwamnatin jihar a zaman majalisar zartaswar yau litinin, gwamnan ya amince a rufe Masallacin kafin kammala sulhun.
Sakatare yada labaran gwamnan, Richard Olabode, ya bayyana cewa an yi hakan ne don samar da zaman lafiya.
Yace:
"Mafita daya da ya rage yanzu shine a rufe Masallacin don a samu zaman lafiya,"
Asali: Legit.ng