Wai Shan Man Fetur Muke yi: Sanusi Lamido Yace Ta Yaya Ake Shan Litan Mai Milyan 66 a Rana
2 - tsawon mintuna
- Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana shakkunsa kan adadin man feturin da ake sha kullum a Najeriya
- Tsohon gwamnan na CBN yace tsakanin 2014 da yanzu adadin man da ake sha ya karu da lita milyan 22
- Sanusi ya yi kira ga gwamnati ta sayar da kamfanin mai na NNPCL kowa ya huta da almundahana
Tsohon gwamnan bankin CBN kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana rashin amincewarsa da ikirarin shan man fetur lita 66m a rana da NNPC tace anayi a Najeriya.
Sanusi ya bayyana cewa ta yaya za'a rika shan wannan adadin man fetur kulli yaumin tun da ba ruwan sha bane.
Tsohon Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Asabar a taron zuba jarin jihar Kaduna KadInvest7.0, rahoton ChannelsTV.
Yace:
"Wai shina shan man fetur muke yi kamar ruwa?"
"NNPC na fada mana cewa mun shan litan mai milyan 66 a rana. Muna sha fiye da Indonesia, Pakistan, Egypt, Cote d’Ivoire, da Kenya."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A 2019, litan mai milyan 40 muke shigowa da shi. Yanzu a 2022, lita milyan 66. Cikin shekaru uku, mun kara yawan shan mai da kashi 50%. Shin adadinmu ne ya kara yawa? motoci ne suka kara yawa? Ka tambayi kan ka, ta yaya hankali zai dauki wannan."
Sanusi ya cigaba da Alla-wadai da kudin tallafin da ake biya idan yayi kira da a sayar da NNPC kowa ya huta saboda babakere wasu yan tsiraru ke da dukiyar Najeriya.
Asali: Legit.ng
Authors: